Kotu Ta Yi Hukunci Kan Korafin Ministan Buhari Kuma Dan Takarar Gwamna a APC

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Korafin Ministan Buhari Kuma Dan Takarar Gwamna a APC

  • Shugabar Kotun Daukaka Kara, Dongban Mensem ya umarci ci gaba da sauraran shari’ar zaben jihar Bayelsa da ake yi
  • Wannan umarni na zuwa ne bayan dan takarar APC a zaben jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya bukaci a rusa alkalan kotun
  • Sylva da jam’iyyarsa ta APC sun zargi alkalan kotun da nuna musu wariya yayin da ake gudanar da shariar kan zaben Bayelsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi fatali da korafin jam’iyyar APC da dan takararta a zaben jihar Bayelsa, Timipre Sylva.

APC da Sylva na kalubalantar yadda ake gudanar da shari’ar zaben jihar inda suka bukaci a rusa mambobin alkalan kotun, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki tsattsauran hukunci kan likitan bogi da ake zargin ya kashe majinyaci

Kotu ta yi hukunci kan bukatar dan takarar gwamnan APC a Bayelsa
Jam'iyyar APC da Sylva na kalubalantar alkalan kotun kan nuna wariya. Hoto: Timipre Sylva.
Asali: Facebook

Wane korafi Sylva da APC ke yi a kotu?

Dan takarar da kuma APC sun zargi alkalan kotun da tauye musu hakkinsu na jin bahasi daga gare su a shari’ar kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin wannan zargi na APC da dan takararta, alkalin kotun, Mai Shari’a, Adekunle Adeleye ya dage sauraran karar ba tare da sanar da lokacin dawo ba.

Har ila yau, shugabar Korun Daukaka Kara ya umarci kotun sauraran shari’ar zaben ta dawo ta ci gaba da sauraran karar a jiya Litinin 11 ga watan Maris.

Yayin zaman kotun, lauyan Sylva, Tunde Falola ya fadawa kotun cewa wanda ya ke karewa ya shigar da korafe-korafe kan alkalan kotun.

Falola ya ce su na zargin kotun da nuna musu rashin adalci tsantsa ba tare da basu damar gabatar da shaidu yadda ya kamata ba, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar na ba da tallafin naira 100,000? An bankado shirin wasu mazambata

Hukuncin alkalin kotun kan korafin Sylva

Sai dai lauyan Gwamna Diri Douye, Chris Uche ya kalubalanci korafe-korafen inda ya bukaci kotun ta yi fatali da su.

Alkalan kotun uku karkashin jagorancin Adekunle sun yi fatali da korafin jam’iyyar APC da kuma dan takararta, Sylva.

Adeleye ya ce shugabar Kotun Daukaka Kara, Dongban Mensem ya umarce su da su ci gaba da sauraran karar a ranar 5 ga watan Maris.

APC, Sylva sun koka kan shari’ar a kotu

Kun ji cewa an takarar gwamna a jihar Bayelsa, Timipre Sylva da jam’iyyar APC sun bukaci a rusa mambobin kwamitin alkalan kotun sauraran shari’ar zaben jihar.

Sylva da APC na zargin alkalan kotun da nuna musu wariya yayin da ake ci gaba da shari’ar zaben jihar Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.