Bayan Dakatar da Betta Edu An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Kori Minista Kan Abu 1 Tak

Bayan Dakatar da Betta Edu An Bukaci Shugaba Tinubu Ya Kori Minista Kan Abu 1 Tak

  • Ƙungiyar lauyoyin Najeriya ta buƙaci kotu da ta soke takardar shaidar NYSC da aka ba Hannatu Musawa da Kenny Ogungbe
  • A ƙarar da ta shigar a kan ministar da Kenny, NBA ta bayyana cewa hidimar ƙasar da Hannatu da Ogungbe suka yi bayan sun haura shekara 30 ta haramta
  • Don haka ƙungiyar ta buƙaci Shugaba Tinubu da ya kori ministar ta al’adu sannan kuma ta buƙaci kotun da ta kiyaye tanade-tanaden dokar NYSC

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) ta sake fito da batun naɗa Hannatu Musawa a matsayin ministar fasaha, al'adu, da tattalin arziƙin fikira da Tinubu ya yi.

A wannan karon dai an buƙaci shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kori Musawa daga muƙaminta bisa zarginta da karya dokar hukumar yi wa ƙasa hidima wato NYSC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dau zafi kan sace shugabanta, ta aike da muhimmin sako ga Tinubu

NBA ta kai karar Hannatu Musawa da Kenny Ogungbe
Hannatu Musawa da Kenny Ogungbe sun yi wa kasa hidima bayan sun haura shekara 30 Hoto: Hannatu Musa Musawa, Kenny Ogungbe GCOB
Asali: Facebook

Sashen NBA kan buƙatun jama’a da dokar ci gaba ya kuma buƙaci kotun da ta tilasta wa hukumar NYSC ta soke takardar shaidar da aka ba Musawa da wani mai tallata waƙa, Kenny Ogungbe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, ƙungiyar ta yi zargin cewa bayar da takardar shaidar ya saɓa wa tanadin dokar NYSC ta Cap N84.LFN 2024.

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da shugaban NBA-SPIDEL, John Aikpokpo-Martins, da sakataren NBA-SPIDEL, Funmi Adeogun, rahoton New Telegraph ya tabbatar.

Musawa, Ogungbe, NYSC, da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya sune wadanda ake tuhuma na farko zuwa na huɗu a cikin ƙarar.

Meyasa aka matsawa Hannatu Musawa?

Batun yi wa ƙasa hidima na ministar ya fara ruruwa ne a watan Agustan 2023, lokacin da hukumar NYSC ta fito ta ce yanzu ministar take yi wa ƙasa hidima.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya aike da muhimmin sako ga Wike da Tinubu bayan nasara a Kotun Koli

Hakan ya janyo kiran da ta yi murabus daga muƙaminta daga wasu sassan ƙasar nan.

Eddy Megwa, daraktan hulda da jama’a na hukumar, ya ce muƙamin minista da da Musawa take riƙe da shi ya saɓa wa dokar NYSC.

Megwa ya bayyana cewa ya saɓa wa dokar NYSC ga duk wani mai yi wa ƙasa hidima ya karɓi muƙamin gwamnati ba tare da ya kammala ba.

Hannatu Ta Nesanta Kanta Daga Magana Kan Batun NYSC

A wani labarin kuma kun ji cewa Hannatu Musa Musawa ta nesanta kanta daga kan martanin da aka rahoto ta yi kan kasancewarta ƴar yi wa ƙasa hidima.

Ministar ta al'adu, fasaha da tattalin arziƙin fikira, ta ce sam wannan martanin ba daga gare ta ya fito ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel