Hanyoyi 6 Masu Sauki da Musulmi Zai Sauke Alkur’ani a Kwanakin Watan Ramadan

Hanyoyi 6 Masu Sauki da Musulmi Zai Sauke Alkur’ani a Kwanakin Watan Ramadan

  • Mafi yawan Musulmai suna son ganin sun haddace Alkur’ani mai tsarki a cikin watan Ramadana sai dai ba su samun dama
  • Mafi yawan wadanda ke gagara sauke Alkur’anin basu samu tsari ba ne yadda za su sauke littafin mai tsarki cikin sauki
  • A wannan rahoton, mun kawo muku yadda Musulmi zai sauke Alkur’ani daga sau daya har zuwa saukewa shida a cikin watan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Yayin da aka shiga watan Ramadan mai alfarma da ake bukatar komawa ga ubangiji, akwai abubuwa da dama da za su taimakawa mutum cimma nasarori.

A watan azumi mafi yawan mutane suke komawa ga ubangiji domin samun yardar Allah tare da yawaita ibada da ambaton Allah domin samun tsira a gobe kiyama, cewar Mishkah Academy.

Hanyar sauke Alkur'ani mai girma cikin sauki a watan Ramadana
Hanyoyin da Musulmi zai sauke Alkur'ani cikin sauki a watan Ramadan. Hoto: Majority World, Anadolu.
Source: Getty Images

Muhimmancin karatu da sauke Alkur'ani a Ramadan

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun kai hari Borno, sun yi barna kafin isowar sojoji

Daga cikin aikin alheri da mutane suka fi yi shi ne karatun Alkur’ani mai tsarki wanda wasu ke samun daman sauke littafin mai tsarki har zuwa karshe yayin da wasu ke ganin zai yi wahala.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malaman Musulunci su na kiran Musulmi da su ninka karatun Alkur'ani mai tsarki musamman a lokacin watan Ramadan domin samun lada da kuma farin ciki sanadin karanata shi.

Malaman sun na kuma horar mabiya da su ci gaba da ayyukan alheri da suke yi a watan Ramadan har zuwa watan saboda dorewa kan tafarki mai kyau.

Yadda Musulmi zai sauke Alkur'ani cikin sauki a Ramadan
Hanyoyi masu sauki da Musulmi zai sauke Alkur'ani cikin azumin watan Ramadan. Hoto: Daniel Beloumou Olomo.
Source: Getty Images

Wannan rahoto zai kawo muku yadda zaku sauke Alkur’ani cikin sauki ba tare da shan wahala ba, kamar yadda Faris Hammadi ya wallafa a shafin X.

Sannan Musulmi zai iya sauke Alkur’anin har sau biyu ko uku ko hudu har zuwa sau shida a cikin watan na Ramadan ba tare da shan wata wahala ba ganin yadda hakan ke da tasiri.

MuslimSG ta jero yadda za ka sauke Alkur’ani a cikin watan Ramadan cikin sauki domin samun albarkar watan:

Jadawalin yadda mutum zai sauke Alkur'ani a Ramadan

Kara karanta wannan

Majalisar shari'ar Musulunci ta goyi bayan rufe makarantu, ta kirayi jihohi 3 su bi sahu

Yawan saukewa a wata

shawan shafuka a kullum

karantawa bayan kowace salla

lokacin da zai dauka

1

shafuka 20

shafuka 4 sau 5

mintuna 4 sau 5

2

shafuka 40

shafuka 8 sau 5

mintuna 8 sau 5

3

shafuka 60

shafuka 12 sau 5

mintuna 12 sau 5

4

shafuka 100

shafuka 20 sau 5

mintuna 20 sau 5

5

shafuka 120

shafuka 24 sau 5

mintuna 24 sau 5

6

shafuka 140

shafuka 28 sau 5

mintuna 28 sau 5

An sanar da ganin watan Ramadan

Kun ji cewa Sarkin Musulmi, Mai Martaba Sa’ad Abubakar III ya sanar da ganin watan Ramdan a daren ranar Lahadi 10 ga watan Maris.

Mai Alfarma Sultan ya bayyana ganin watan ne bayan rahotanni da aka samu na ganin watan a bangarori da dama a jihohin Najeriya inda ya yi fatan alheri ga al'ummar Musulmin kasar.

Wannan sanarwar ita ke tabbatar da fara azumin watan Ramadan wanda aka yi a ranar Litinin 11 ga watan Maris wanda zai dauki tsawon kwanaki 29 ko 30.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.