'Yan Ta’adda da Makiyaya Ne Ke Jawo Wahalhalun da Ake Sha a Najeriya, Inji Fasto Ayodele
- Babban fasto a Najeriya ya bayyana kadan daga tushen matsalolin Najeriya da yadda za a shawo kansu
- Ya yi tsokaci da cewa, makiyaya da ‘yan ta’adda ne silar lalacewar tattalin arzikin kasar nan baki daya
- Ya shaida cewa, ya kamata gwamnati ta sanya hukuncin kisa kan duk wanda aka kama da laifin ta’addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Najeriya - Shugaban cocin INRI, Primate Elijah Ayodele, ya yi ikirarin cewa halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya ba komai bane face sakamakon ayyukan kashe-kashe da ‘yan ta’adda da makiyaya ke yi.
Primate Ayodele wanda ya yi magana a ranar Alhamis ya ce idan Gwamnatin Tarayya ta yi amfani da hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin, to dole tattalin arzikin zai farfado.
A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai Oluwatosin Osho ya fitar, Ayodele ya soki wasu masu fada a ji da suka shiga tsakani wajen kawo cikas ga kame ‘yan ta’adda, New Telegraph ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bayanan fasto Ayodele kan rashin tsaro
A cewar Ayodele:
“Yaki da yanayin tattalin arzikinmu ba shine mafi kyawun abin da za mu yi ba; muna da albarkatu a kasar nan, ba za mu iya amfani da su ba?
“Muna bukatar sake fasalin tattalin arzikinmu ta yadda kowace jiha za ta sarrafa albarkatunta domin tattalin arzikin ya daidaita.
"Kasar nan na iya samun kudi daga albarkatu masu yawa. Muna da albarkatu a jihohi kamar Taraba, Zamfara, Borno, Kogi da sauransu. Akwai abubuwan da yawa da shugaban kasa ya kamata ya yi don daidaita tattalin arzikin kasar.
“Rashin tsaro da ‘yan ta’adda da makiyaya masu kisa suka haifar na daya daga cikin abubuwan da ke jawo wahalhalu. Kamar yadda na fada a baya, ya rattaba hukuncin kisa ga duk wani dan ta'adda da aka kama.
Sojoji na kokari, amma ana kawo masu tsaiko, inji fasto Ayodele
Ya kuma bayyana yadda sojoji ke kokarin kame ‘yan ta’adda a kasar nan, amma ake samun wasu masu fada a ji da ke shiga tsakani don kawo cikas, rahoton Daily Post.
A cewarsa:
“Rundunar sojojin Najeriya za ta iya yakar ‘yan ta’adda, ku ba su duk abin da suke bukata, nan ne za ku ga idan muka samu isasshen wutan lantarki, an rage ayyukan ‘yan ta’adda, za a samu wadataccen abinci da za mu ci.”
Manyan matsalolin Najeriya rashin tsaro ne, gwamna Sani
A wani labarin, Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da ke fuskantar Najeriya a halin yanzu.
Uba Sani ya ce shugabanni siyasa a kasar sun biyo hanyar da ba daidai ba wajen kawo karshen wadannan manyan kalubalen guda biyu.
Gwamnan ya yi wannan jawabi ne a wajen taron zaman lafiya tsakanin mabiya addinai karo na shida tare da hadin gwiwar gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng