Kungiyar IPC Ta Tara ‘Yan Jarida Daga Jihohin Arewa Ta Horas da Su a Kaduna

Kungiyar IPC Ta Tara ‘Yan Jarida Daga Jihohin Arewa Ta Horas da Su a Kaduna

  • Kungiyar IPC da ke garin Legas ta shirya taro na musamman inda aka horar da kananan manema labarai
  • ‘Yan jarida daga jihohin Arewa maso yamma da Arewa maso tsakiya sun karu da sanin kayan aiki da FOI
  • Wannan yana cikin shirye-shiryen EUSDGN da kungiyar kasashen Turai watau EU ta fito da su a duniya

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - An yi kira ga manema labarai da su rungumi amfani da na’urori da kayan aikin zamani wajen kawar da labaran bogi.

Kungiyar IPC ta ‘yan jaridar Duniya da ke garin Legas tayi wannan kira a wajen wani taron karawa juna sani a garin Kaduna.

Kungiyar IPC
'Yan jarida wajen taron IPC a Kaduna Hoto: @IPCng
Asali: Twitter

IPC/EUSDGN sun bada horo na musamman

IPC da hadin-kan tsarin EUSDGN na kungiyar nahiyar Turai (AU) ta shirya taro musamman domin horar da ‘yan jarida.

Kara karanta wannan

Gaza: Bam ya kashe ‘yanuwa 36 lokacin shirin sahur a dauki azumin Ramadan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabin da ta gabatar a madadin kungiyar, Stella Nwofia tayi kira ga mahalartan da su yaki masu yada labarain bogi da karya.

An kuma bukaci manema labaran suyi amfani da dokar FOI wajen samun bayanai daga gwamnati, kungiyoyi da kamfanoni.

IPC ta shirya taron ne domin masu aikin jarida, tashoshin rediyo, gidajen talabijin a jihohin Arewa maso yamma da na tsakiya.

Manufar IPC a taron da aka yi ranar Laraba da Alhamis ita ce nunawa ‘yan jarida yadda za a bankado gaskiya a rahotanni.

IPC da kayan zamani a aikin jarida

Lanre Arogundade wanda shi ne shugaban IPC ya wayar da kan ‘yan jaridan game da yadda za su ci moriyar na’urorin zamani.

Idan ana amfani da wadannan kayan aiki, za a iya bankado karyar da ake yi da sunan yada labarai a duniyar nan da ake ciki.

Kara karanta wannan

Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Ambasada Bawa ya riga mu gidan gaskiya a Abuja, bayanai sun fito

Yadda 'yan jarida suka samu gogewa

Malam Umar Namadi wanda ya halarci taron ya ce ya karu sosai kuma an yi masa allurar zaburarwa a fagen bincike a aikin jarida.

Bugu da kari, ‘dan jaridar ya shaidawa Legit ya samu damar haduwa da kwararrun abokan aiki daga ko ina da za su taimaka masa.

Shi kuwa Abdullahi I. Adam ya ce bayan ilmin da ya samu, ya ci karo da wadanda suka goge.

A wajen wannan taron karawa juna sani, ‘dan jaridar ya fahimci abubuwa birjik, kuma zai maida hankali a kawo labaran gaskiya.

Kungiyar IPC ta bada horo a kan FOI

Edetaen Ojo, shugaban Media Rights Agenda ya bude idon mahalartan da dokar FOI da Goodluck Jonathan ya sa wa hannu a 2011.

Wannan zai taimakawa bibiyar alkawuran da ‘yan siyasa suke yi wa al’umma lokacin kamfe domin ana zarginsu da karya.

Dr. Fatima Omone Shu’aibu ta gabatar da Makala a taron, ta ankarar da mahalartan 40 a kan rahotanni game da jinsi a labarai.

Kara karanta wannan

Tinubu na fuskantar sabuwar matsala yayin da 'yan fansho ke shirin fita zanga-zanga tsirara

Karin albashin ma'aikata

Kwanaki kun samu labari cewa NLC ta ce an yi mata barazana iri-iri domin a yi watsi da gama-garin zanga-zangar da ta shirya.

Joe Ajaero yake cewa sun ci karo da duk wani nau’in matsin lamba da barazana daga mahukunta saboda a ga bayan kungiyar NLC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng