"Abubuwa 4 da Tsohon Shugaba Jonathan Ya Yi da Ba Za a Maimaita Su Ba", Shehu Sani

"Abubuwa 4 da Tsohon Shugaba Jonathan Ya Yi da Ba Za a Maimaita Su Ba", Shehu Sani

  • Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan, ya cika shekara 66 a duniya a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamban 2023
  • Jonathan, wanda ya zama shugaban Najeriya daga 2010 zuwa 2015, an haife shi a shekarar 1957 a jihar Bayelsa
  • A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Sanata Shehu Sani ya yi nuni da abubuwa aƙalla guda hudu da ya ce Jonathan ya yi a lokacin mulkinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya faɗi abubuwa huɗu da ya ce tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya yi "waɗanda wani shugaban ƙasa ba zai sake maimaita su nan gaba kaɗan ba."

Sani a wani rubutu da ya yi a soshiyal midiya a ranar Litinin, 20 ga watan Nuwamba, ya taya Jonathan murnar zagayowar ranar haihuwarsa yayin da tsohon shugaban ƙasan ya cika shekara 66.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Yadda Atiku da Obi za su kayar da Tinubu a zaben 2027

Shehu Sani ya yabi Goodluck Jonathan
Shehu Sani ya taya Jonathan murnar zagayowar ranar haihuwarsa Hoto: Shehu Sani, Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

"Barka da zagoyowar ranar haihuwa Goodluck Jonathan": Shehu Sani

Shehu Sani ya rubuta a shafinsa na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Akwai abubuwa guda huɗu da tsohon shugaban ƙasa Jonathan ya yi wadanda wataƙila wani shugaban ƙasa ba zai sake maimaita su nan gaba ba, naɗa shugaban INEC da bai taba sani ba kuma ba su taɓa haɗuwa ba. Ya yarda da amfani da tsarin tattara bayanai a zaɓen da ya kai ga korar shi daga mulki. Ya buƙaci ɗan takarar jam'iyyar adawa ya zaɓi kwamishinan INEC ɗaya. Bai yarda da sakamakon zaɓe ba amma ya taya wanda ya ci nasara murna domin a samu zaman lafiya da haɗin kan ƙasa."
"Ga masu son zaman lafiya shi mutum ne mai son zaman lafiya, ɗan ƙasa na gaskiya kuma mai kishin ƙasa, ga masu son tada rigima, ya kasance mutum mai kawo cikas. GEJ ya ceci ƙasar nan a cikin lokacin da take cikin mawuyacin hali."

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Babban malamin addini ya yi magana kan yiwuwar tsige Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa

"Barka da zagayowar ranar haihuwa tsohon shugaban ƙasa Goodluck."

Manyan abubuwa 4 Jonathan ya yi - Sani

1. Ya naɗa shugaban hukumar zaɓe mai zaman ƙanta ta ƙasa (INEC) wanda bai taɓa saninsa ba kuma bai taɓa haɗuwa da shi ba.

2. Ya amince da amfani da tsarin tattara bayanai a zaɓen da ya kai ga raba shi daga ƙaragar mulki.

3. Ya buƙaci ɗan takarar jam'iyyar adawa ya zaɓi kwamishinan INEC ɗaya.

4. Bai yarda da sakamakon zaɓe ba amma ya taya wanda ya lashe zaɓe murna domin samun zaman lafiya da haɗin kan ƙasa.

Sylva Ya Caccaki Jonathan

A wani labarin kuma, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APC a zaɓen jihar Bayelsa, Timipre Sylva ya caccaki tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan.

Sylva ya caccaki Jonathan bayan ya ce da ya lashe zaɓen gwamnan jihar da ya mayar da mahaifiyarsa zuwa birnin tarayya Abuja da zama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel