Young Sheikh: Malami ‘Dan Shekara 11 Ya Dauko Yunkurin Hada Kan Malaman Musulunci
Muhammad Zakir Shamsuddeen watau Young Sheikh yana yawon hada-kai tsakanin malamai da ke sabanin fahimta
Malamin da ake yi wa kallon yaro yana jin haushin yadda musulmai da suka yi imani da Annabi SAW suke kafirta junansu
Young Sheikh ya kai ziyara wajen Maula Sheikh Dahiru Usman Bauchi da irinsu Sheikh Halliru Maraya a ‘yan kwanakin nan
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Kaduna - Muhammad Shamsuddeen wanda aka fi sani da Young Sheikh ya dage wajen hada-kan al’ummar musulman kasar nan.
Kokarin Muhammad Shamsuddeen shi ne yadda za a ajiye bambace-bambace, a kuma daina kafirta juna saboda sabanin fahimta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyara da yunkurin Young Sheikh
Malamin ya kai ziyara gari zuwa gari domin zama da sha’irai, sharifai, shehunnai da manyan waliyyai da darikunan musulunci.
Bayanai sun nuna Young Sheikh ya samu albarkar Sayyada Fatiha Chota wanda jika ce ga Shehu Ibrahim Inyass da Shehu Chota.
Bidiyo a shafin Youtube da Tik Tok sun nuna ziyarar da ya kai wajen Sayyada Dr. Zahra'u Niass wanda ta yaba da irin baiwarsa.
Wannan malama ta ga karamomi na malanta wajen wannan yaro mai shekaru 11, tace ba a saba ganin irin haka a duniya ba.
Bayan ziyarar da ya kai wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya kuma gana da ‘ya ‘yan shehin irinsu Sayyadi Baffa Dahiru Bauchi.
Legit ta samu labari malamin ya hadu da Khalifa Shehu Mahi Inyass, Sarkin Sharifai na Gusau da Sarkin Zakirai na Nasarawa.
Sheikh Halliru Maraya mai kokarin hada-kan jama'a, Malam Mai Barota, Musa Chota duk sun sa albarka a tafiyar Young Sheikh.
Young Sheikh ya je wajen Nur Khalid a Abuja
Muhammad Shamsuddeen ya gana da limamin nan na Abuja, Muhammad Nur Khalid, a baya ya nemi su hadu, ba a dace ba.
Nur Khalid ya ce kyau a daina kallon shekarun Young Sheikh, a rika duba baiwarsa
Malamin mai tasowa ya ce tun da Sheikh Ibrahim Inyass ya kai ziyara wajen kafirai, babu abin da zai hana a ziyarci sauran malamai.
Malam Young Sheikh a wajen shehunnai
Ya ziyarci Sheikh Alawy Kano, Shehu Mansur Imam, Sheikh Muhammad Suru, Khalifan Mai Ishiriniya Kano da Tanimu Mai Rawani.
Bayan wa’azi da ya yi har a Nijar, Young Sheikh ya je wajen Sheikh Bello Yabo duk saboda a ajiye bambanci, a bautawa Allah SWT.
A lokacin da ya hadu da Sheikh Nuhu Tahir Tajuddeen, ya samu damar ganawa da Alkali Ustaz Abubakar Salihu Zaria a garin Zariya.
Mecece manufar Young Sheikh?
Mahaifinsa, Malam Shamsuddeen Aliyu Maiyasin ya shaida mana tun Young Sheikh yana shekara 7 ya hardace Al-Kur’ani mai tsarki.
A yanzu yana shekara 11 a duniya kuma tun shekarar 2021 ya fara yin karatun tafsiri, kwanaki aka rahoto cewa mahafiyarsa ta rasu.
Shamsuddeen Aliyu Maiyasin ya fadawa Legit burin yaron shi ne ganin musulmai sun daina kafirta juna a dalilin sabanin nasu.
Kur'anin kurame a Zariya
A wata hira da Ustaz Yasir Sulaiman Kofa, kuna da labari ya shaida mana yadda suke koyawa kurame karatun Kur’ani mai tsarki.
Malamin ya ce sun fara aikin koyarwar ne da niyyar da’awa, daga baya aka shiga ilmin Littafi mai tsaki domin masu larurar ji.
Asali: Legit.ng