Yanzu-yanzu: An nada Sheikh Nuru Khalid limanci a sabon Masallaci a Abuja

Yanzu-yanzu: An nada Sheikh Nuru Khalid limanci a sabon Masallaci a Abuja

Abuja - Limamin Masallacin da aka kora a rukunin gidajen yan majalisu dake birnin tarayya Abuja, Sheikh Nuru Khalid, ya samu sabon limanci a masallacin Juma'a.

Kwamitin wata Masallacin Juma'a dake bayan rukunin gidajen babban bankin tarayya CBN dake Abuja ta nada shi, rahoton TheNation.

Ranar Juma'a, 18 ga Afrilu zai fara jagorantar jama'a a Masallacin.

Sheikh Nuru Khalid
Yanzu-yanzu: An nada Sheikh Nuru Khalid limanci a sabon Masallaci a Abuja Hoto: Al Afriky
Asali: Twitter

Sheikh Khalid yace:

"Da yardar Allah zan fara jagoranci a sabon Masallacin ranar Juma'a, saboda a matsayinmu na Malamai muna bukatan wajen ibada."
"Akwai Masallacin Juma'an da muka gina bayan CBN Quaters a Abuja; can zan fara limancin yanzu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel