Sheikh Dahiru Bauchi Na Fama Da Rashin Lafiya, An Aika Masa Da Gaisuwa

Sheikh Dahiru Bauchi Na Fama Da Rashin Lafiya, An Aika Masa Da Gaisuwa

  • Mutane sun cika addu'a yayinda labarin rashin lafiyan Sheikh Dahiru Bauchi ya karade soshiyal Midiya
  • Shehi wanda dan asalin jihar Bauchi ne yana gudanar da Tafsirin Al-Qur'ani a jihar Kaduna
  • Babban Malamin ya kwashe gomman shekarun rayuwarsa yana karantar da jama'a ilmin addini

Jagoran mabiya darikar Tijjaniya a yammacin Afrika kuma babban Malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, yana fama da rashin lafiya.

Dan takaran shugaban kasa karkashin lemar jam'iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar ya bayyana hakan a sakon gaisuwar da ya aikewa babban Malamin.

Ya bayyana kaduwarsa sosai bisa labarin rashin lafiya Shehi kuma ya yi addu'an Allah ya bashi lafiya.

Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Bauchi Na Fama Da Rashin Lafiya, An Aika Masa Da Gaisuwa Hoto: Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A jawabin da ya fitar a shafinsa na yanar gizo, Atiku Abubakar ya bayyana muhimmancin Sheikh Dahiru Bauchi ga al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Kara Shiga Tasku, Wani Jigo Da Ya Nemi Takarar Gwamna a APC Ya Koma PDP

A cewarsa:

"Na samu labarin da ya taba min zuciya sosai na cewa shugaban darikar Tijjaniyya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi yana fama da rashin lafiya."
"Dubi ga irin jagorancinsa da kuma alakar Shehi da al'ummar kasar, ina aike masa da addu'o'in Allah ya bashi lafiya."
"Allah ya kara sauki Sheikh Dahiru Bauchi kuma Allah ya cigaba da kareka don amfani da kake yiwa al'umma."

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel