Yan Najeriya na farin ciki da rufe iyakar kasar - Buhari

Yan Najeriya na farin ciki da rufe iyakar kasar - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yan Najeriya sun yi farin ciki da shawarar da gwamnati ta dauka na rufe dukkan iyakokinta, inda ya dage kan cewa matakin ya taimaka wajen biyan bukatar hazikan yan kasa masu sarrafa kaya.

Ya bayyana cewa shawarar ya kasance matakan bunkasa yan Najeriya masu sarrafa kaya, "sun kuma yi farin ciki saboda ta hakan ne muka kau da kayayyaki masu cutar da lafiyarmu wadanda ake shigowa dasu kasar."

Ya yi maganan ne ta bakin Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a taron ranar abinci na duniyya wacce kungiyar mata na kasa ta shirya a Abuja.

Ya jaddada cewa rufe iyakar bai tsayar da kasuwanci da kasashen ketare ba kawai ya inganta kasuwanci mai daraja ne.

Ministan kula da harkokin mata Pauline Tallen wacce tayi magana a taron, ta bayyana cewa taron ne hanyar hada kai da sauran kasashen duniya don murnar bikin ranar matan karkara na duniya.

Ta nuna yakinin cewa taron zai kara inganta tunanin cewa mata ne tushen shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya akan fannin noma da gina yankunan karkara.

KU KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi martani akan gobarar Onitsha

Shugaban kungiyar mata ta kasa, Laraba Shoda tace taron ranar abinci na duniya ya nuna muhimmancin abinci a rayuwar dan adam.

Ta kara da cewa taron ya zama kamar gangami ga dukkan masu ruwa da tsaki kan su mayar da hankali wajen cimma nasarar samar da abinci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng