Bayan Shafe Shekaru 5 a Turai, Matashi Ya Tattara Kudinsa, Ya Gina Dankareren Gida a Mahaifarsa

Bayan Shafe Shekaru 5 a Turai, Matashi Ya Tattara Kudinsa, Ya Gina Dankareren Gida a Mahaifarsa

  • Wani matashi da ya shafe tsawon shekaru biyar yana buga-buga a kasar Birtaniya, ya yi nasarar kewarawa kansa gida
  • Da yake baje kolin katon gidan da ya gina, mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu a sashin sharhi
  • Wasu 'yan tsirarun mutane na ganin mallakar gidan kasa bayan shafe shekaru biyar a Birtani bai yi ba, amma ya ba su amsa daidai da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani matashi 'dan Najeriya da ke zama a UK ya yi bidiyon gidan da ya yi nasarar samu daga shekaru biyar d aya yi a turai.

Mutumin (@lil.carmas.uk) ya tura kudi gida don a gina masa hadadden gida. Bidiyon nasa ya hasko yadda aikin ginin ke gudana.

Kara karanta wannan

Yara 35 nake sha'awa kuma na so kara mata 3 Inji wanda ya auri mata 3 a rana 1

Ya tura kudaden da ya tara gida don a yi masa gini
Ya gina gidan ne a kasarsa Hoto: @lil.carmas.uk
Asali: TikTok

Hadadden gidan gidan kasa

Har ma ya nuna tsarin ginin da ya yi amfani da shi. Kowane kusurwa na gidan yana da ginshikan da za su iya jure nauyin ginin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gidan mutumin na dauke da dogon rufin kwano wanda mutane da dama ke ganin ya fi dadewa saboda yana da gangara.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

kxngfamo ya ce:

"Na tayaka murna!! Kada ka kula makiya da ke sashin sharhi. A hankali a hankali har ka gama! Ka yi iya abin da za ka iya!"

lil_slae_01:

"Abinci ni nake ci da nawa kudin."

skipper:

"Na tayaka murna amma dai akalla ka kammala gidan kafin ka wallafa shi."

Nono Blackbunny:

"Sannu da kokari ba abu mai sauki bane."

AWOBONA:

"Ba laifi amma dai shekaru 5 ya cancanci fiye da gidan kasa."

Kara karanta wannan

Tsoho mai shekara 85 ya shiga hannu a Kano bisa zargin garkuwa da ‘dan Shekara 3

uza ya tambaya:

"Tsawon shekaru 5 a Birtaniya amma wannan ne abin da ka iya samu?"

Budurwa ta kera gida tana da shekaru 20

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta cimma muradionta na gina gida da zama mai gidan kanta tun tana da kuruciyarta.

Matashiyar ta dauki hoto a gaban gidan da aka kammala gininsa tare da iyayenta yayin da ta kasance rike da takardun gidan.

Wani bidiyon TikTok da kanwarta @everythinglabam0 ta wallafa, an gano matashiyar tana zagaya cikin harabar gidan don nuna jin dadinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel