Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Sama da 15, Sun Tafka Mummunar Ɓarna Ana Dab da Azumi a Jihar Arewa
- Yan bindiga sun kashe bayin Allah da dama ciki har da ƙaramin yaro a yankin karamar hukumar Gwer ta jihar Benuwai
- Rahoto daga mazauna yankin ya nuna cewa maharan sun ƙona gidaje da yawa yayin harin da suka kai ranar Alhamis da daddare
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Benuwai, Catherine Anene, ta ce har kawo yanzu ba ta samu rahoto kan faruwar lamarin ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - Wasu miyagun ƴan bindiga sun halaka mutane 17 yayin da suka kai farmaki kauyen Mbaikyor Mbalom da ke ƙaramar hukumar Gwer a jihar Benuwai.
Wata majiya a cikin al’ummar kauyen ta tabbatar da haka ga jaridar The Cable, ta ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyen a daren ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, 2024.
Ya kara da cewa a yayin harin ƴan bindigar sun kona gidaje da dama kafin su kashe mutanen da babu ruwansu, ciki har da wani ɗan karamin yaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar majiyar, sai washe gari yau da safiyar Jumu'a, mazauna kauyen suka samu damar ɗauko gawawwakin waɗanda aka kashe, rahoton The Nation.
"Ƴan bindigar sun kai hari gidana da ke gundumar Mbaikyor Mbalom a karamar hukumar Gwer ta jihar Benuwe,” in ji majiyar.
Sunayen waɗanda maharan suka kashe
Ya jero sunayen mutanen da aka kashe da suka haɗa da, Peter Tion, Nyityo Kyyoon, Iorfa Ukombor, Doopinen Awua, Tyoshaa Mkaanem, Asan Ate, Asough Ate, Igba Byuan da Master Ter Byuan.
Sauran su ne Terzungwe Asoo Ate, MWO Mbatsavbun Gbatar (mai ritaya), John Ndahagh Tyohemba, Tertsea Ukombor, Akuma Kpenge, Abume Kpenge, Terzungwe Aulugh da wani karamin yaro.
Ba mu da masaniya kan lamarin - Yan sanda
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Benue, Catherine Anene, ta ce ba ta da masaniya kan lamarin. "Ba ni da wannan bayanin,” in ji Anene.
A baya-bayan nan, mutane da dama ne suka rasa rayukansu a wata arangama da aka yi tsakanin kungiyoyin ‘yan bindiga a karamar hukumar Ukom ta jihar Benuwai.
Cutar ƙyanda ta ɓarke a makarantu a Kuros Riba
A wani rahoton kuma Gwamnatin jihar Kuris Riba ta tabbatar da ɓarkewar cutar kyanda a wasu makarantu biyu a ƙaramar hukumar Akpabuyo.
Rahoto ya nuna cewa bullar cutar ya tilastawa makarantun tafiya hutun dole yayin da gwamnati ta fara yunƙurin kawar da cutar.
Asali: Legit.ng