"Mijina Ya Daina Kwana da Ni" Matar Aure Ta Cire Kunya Ta Fashe da Kuka a Gaban Kotu
- Dirama a wata kotu a Ilorin yayin da matar aure, Aminat ta fashe da kuka kan abubuwan da mijinta ke mata a gidan aure
- Matar ta shaidawa alkali cewa mijinta mai suna, Isma'il Gobir, ya ƙauracewa gadon sunnah, ba ya kula da ita da yaran da suka haifa
- Sai dai magidancin ya nemi a ba shi lokaci ya sasanta da uwar ƴaƴansa, kotu ta ɗage zaman zuwa ranar 20 ga watan Maris
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ilorin, Kwara - An yi ƙaramin wasan kwaikwayo a Kotun yanki da ke Centre-Igboro, Ilorin, babban birnin jihar Kwara ranar Alhamis lokacin da wata matar aure, Aminat Nagode-Allah ta fashe da kuka.
Matar dai ta fashe kuka a gaban alkali yayin da take ƙorafin mijinta ya ƙaurace ma gadon aurensu na Sunnah, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Aminat ta garzaya kotun ne tana neman ta rabu da mijinta, Ismail Gobir, bisa dalilin rashin soyayya da kuma gaza sauke nauyinta da yaran da suka haifa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shigar da ƙarar ta gaza riƙe kanta yayin da take bayanin yadda mijinta ya ƙauracewa gadon aurensu na tsawon watanni, nan take sai gani aka yi ta fashe da kuka.
"Bai damu da yadda nake ji ba, ya daina tambayar daga ina nake samun abincin da nake dafawa a gidan, kawai shi dai a dafa ya ci abinci ya fice kullum.
"Ya watsar da gadon aurenmu, ya bar mana ni da yara, yanzu ya koma kwana a kan kujera a falo, ba tare da ya ji sha'awar kwanciya da ni ko kulawa ba.
“Ina fafutukar sayar da Garri, har ma wani lokacin sai na je neman rancen kudi domin in ciyar da gidan, amma mijina bai damu da ya san ya nake yi ba."
- Aminat Nagode-Allah.
Saboda waɗannan dalilin Aminat ta roƙi kotun ta raba aurensu wanda aka ɗaura bisa shari'ar Musulunci, kamar yadda Daily Nigerian ta rahoto.
Magidancin ya ƙi aminta da raba auren
Da yake jawabi, Gobir ya shaida wa kotu cewa yana fuskantar wasu matsaloli ne a harkokin kasuwancinsa, wanda hakan ya sa ba zai iya ciyar da iyalin ba
Duk da ya aminta da kwazo da kokarin da matarsa take yi wajen ciyar da gidansu, ya zarge ta da dawowa gida a makare da kuma amsa kiran waya da yawa.
Magidancin ya ce har yanzu yana da sha’awar auren, kuma ya roki a ba shi lokaci domin ya samu damar sasantawa da matarsa.
Wane mataki kotu ta ɗauka?
Alkalin kotun, Hammad Ajumonbi, ya zargi wanda ake kara da barin gadon aurensa da rashin soyayya da sha'awar matarsa.
Ajumonbi ya fadawa matar da ta kara hakuri da juriya domin duk aure yana da kalubale, sannan ya ɗage zamam zuwa 20 ga watan Maris.
Magidanci ya koka da halin matarsa a turai
A wani rahoton kuma wani magidanci da ya koma Birtaniya tare da matarsa a yanzu ya yi nadamar hakan saboda matar tana cin amanarsa.
An ce mutumin ya kashe sama da Naira miliyan 30 wajen tabbatar da bizarsu, amma matar hankalinta ya koma wajen tsohon saurayinta.
Asali: Legit.ng