Kungiyar Izala Ta Yi Martani Kan Hallaka Malamin Musulunci, Ta Tura Sakon Gargadi
- Yayin da ake jimamin kisan gillar da aka yi wa Sheikh Hassan Mada a Zamfara, kungiyar Izala ta yi martani kan lamarin
- Kungiyar ta zargi jami'an CPG da hannu a kisan da aka yi wa shugaban majalisar malaman birnin Gusau da ke Zamfara
- Wannan na zuwa ne bayan kama wasu 'yan banga 10 da zargin su na da hannun a kisan da aka yi wa shehin malamin a jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Kungiyar Izala reshen jihar Zamfara ta zargi wasu daga jami'an CPG da hannu a kisan Sheikh Abubakar Hassan Mada.
Kungiyar ta yi wannan zargi ne a yau Juma'a 8 ga watan Maris ta bankin shugabanta, Alhaji Aliyu Zurmi.
Menene martanin kungiyar kan kisan malamin?
Wannan na zuwa ne bayan kisan Sheikh Abubakar Hassan Mada wanda shi ne shugaban majalisar malamai na birnin Gusau, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin sanarwar da kungiyar ta fitar, ta bayyana wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da hannun wasu jami'an hukumar a kisan gillar.
Har ila yau, kungiyar ta tabbatar da bayanin Kwamandan hukumar, Kanal Rabi'u Yandoto inda ya ce akwai hannun wasu jami'ansa a kisan.
"Muna kira ga kakakin gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris da ya janye kalamansa inda ya ke kare wandanda ake zargi da kisan."
"A matsayinmu na kungiyar Musulunci, muna kiransa da ya ji tsoron Allah a ayyukansa saboda akwai ranar da zai tsaya a gaban Allah."
- Aliyu Zurmi
Kungiyar ta shawarci al'umma kan daukar doka
Har ila yau, kungiyar ta ce duk da abin takaicin da ya faru, ta na kira ga al'umma da su guji daukar doka a hannunsu inda ta ce za ta bi duk hanyar da ta dace domin daukar mataki.
Yayin da take Allah wadai da kalaman kakakin gwamnan, kungiyar ta shawarce shi da ya yi hankali yayin gudanar da ayyukan da aka saka shi musamman a irin wannan yanayi.
An kama wadanda suka hallaka Sheikh Mada
A baya, mun ruwaito muku cewa, gwamnatin jihar Zamfara ta sanar da cafke mutane 10 da zargin kisan Sheikh Abubakar Hassan Mada.
Gwamnatin ta ce daga cikin wadanda aka kama akwai 'yan banga amma ba jami'an hukumar CPG ba ne.
Asali: Legit.ng