Tambuwal Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa, Ya Tunatar Masa Halin da Aka Shiga

Tambuwal Ya Ziyarci Tsohon Shugaban Kasa, Ya Tunatar Masa Halin da Aka Shiga

  • Yayin da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ke cika shekaru 87, Aminu Tambuwal ya taya shi murnar zagayoyar ranar haihuwa
  • Sanata Tambuwal ya kuma sake tunatar da tsohon shugaban Najeriyan halin da ‘yan kasar ke ciki inda ya ce kullum kara gaba yake yi
  • 'Dan majalisar dattawan ya bayyana haka ne a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun jim kadan bayan ya gana da tsogon shugaban kasar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya samu ganawa da tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a gidansa da ke jihar Ogun.

Tambuwal wanda ke wakiltar Sokoto da Kudu ya bayyana wa Obasanjo irin halin da kasar ke ciki na matsaloli da dama.

Kara karanta wannan

Buga kudi: Yadda Buhari ya jawo hauhawar farashin kaya, Ministan Tinubu ya magantu

Tambuwal ya fada wa tsohon shugaban kasa halin da yanzu ake ciki a Najeriya
Tambuwal ya taya Obasanjp murnar cika shekaru 87 a duniya. Hoto: Olusegun Obasanjo, Aminu Waziri Tambuwal.
Asali: Facebook

Me da mene Tambuwal ya fadawa Obasanjo?

Sanatan ya bayyana haka ne a birnin Abeokuta da ke jihar Ogun jim kadan bayan ya gana da tsogon shugaban kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasar, Kahinde Akinyemi ya fitar, cewar Daily Trust.

Kahinde ya ce Tambuwal ya kai ziyarar ce don taya Obasanjo murnar cika shekaru 87 a duniya.

Sanata Tambuwal ya bukaci ‘yan Najeriya da su kasance masu addu’a ga kasar da kuma sa ran zata fita daga kangin da take ciki.

“Zan yi kira ga Shugaba Tinubu ya sani cewa ana cikin wani hali a Najeriya, ya kamata ya saurari koken ‘yan kasar.
“Yan Najeriya suna cikin wani irin hali wanda basu taba shiga ba, ya nemi shugabancin kuma ya samu, ya kamata ya yi abin da ya dace.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Fitaccen basarake ya tura sako ga Tinubu kan kafa hukumar kayyade farashi

- Aminu Tambuwal

Tambuwal ya kwarara yabo ga Obasanjo

Tambuwal ya ce ya zo musamman har jihar Ogun kamar yadda yake zuwa ko wace shekara domin taya shi murna, cewar Daily Post.

“Na zo har birnin Abeokuta kamar yadda na saba yi a kullum domin taya Baba murnar zagayoyar bikin ranar haihuwarsa.
“Tabbas ya kasance shugaban nagari ba iya Najeriya ba hatta duniya baki daya kuma wanda muke koyon abubuwa da dama daga gare shi.”

- Aminu Tambuwal

Obasanjo ya shawarci Tinubu

Kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo ya shawarci Shugaba Tinubu yadda zai kawo karshen tashin farashin kaya.

Obasanjo ya ce ganin yadda Zimbabwe ta shiga irin wannan hali kuma ta yi nasarar fita, ya kamata Tinubu ya tuntubi kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.