Kungiyar Kwadago Ta Mika Sabuwar Bukata Ga Gwamnati Game da Mafi Karancin Albashi
- Rahotanni na nuna cewa kungiyar kwadago za ta nemi N500,000 a matsayin mafi karancin albashi ga ma'aikatan Najeriya
- A yayin da za a fara taron jin ra'ayin jama'a na shiyya-shiyya kan sabon tsarin albashi a yau (Alhamis), kungiyar za ta yanke matsayarta
- Kungiyoyin kwadago, gwamnonin jihohi, ministoci, kungiyoyin farar hula,ne za su yanke hukunci kan sabon mafi karancin albashin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Rahotanni na nuna cewa kungiyar kwadago za ta nemi N500,000 a matsayin mafi karancin albashi yayin da za a fara sauraron ra'ayoyin jama'a kan sabon tsarin albashin.
A ranar Alhamis (yau) ne za a fara taron jin ra'ayin jama'a na shiyya-shiyya kan sabon tsarin albashi a Legas, Kano, Enugu, Akwa Ibom, Adamawa, da Abuja.
NLC za ta nemi N500,000 a taron na yau
A ranar 11 ga watan Fabrairu ne shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Joe Ajaero, a wata hira da Arise TV, ya bayyana cewa kungiyar kwadago za ta nemi naira miliyan 1 matsayin mafi karancin albashi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai wani babban jami’in kungiyar ta NLC, wanda ya zanta da jaridar The Punch a ranar Alhamis ya ce kungiyar za ta nemi N500,000 ne kawai a taron na yau.
Arise News ta ruwaito cewa a lokaci guda ne za a gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a kan sabon mafi karancin albashin a dukkan shiyyoyi shida na kasar.
Jerin wadanda za su jagoranci taron jin ra'ayoyin
Kungiyoyin kwadago, gwamnonin jihohi, ministoci, kungiyoyin farar hula, da kungiyoyi masu zaman kansu ne za su yanke hukunci kan sabon mafi karancin albashin.
PUNCH ta samu labarin cewa shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya Joe Ajaero ne zai jagoranci taron a yankin arewa maso gabas da ke gudana a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Ministan kudi kuma ministan tattalin arziki, Wale Edun ne zai jagoranci zaman sauraren ra'ayoyin a yankin Kudu maso Yamma da ke gudana a Legas.
Tinubu ya kaddamar da kwamitin mutum 37
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya kaddamar da kwamitin mutane 37 kan sabon mafi karancin albashi a a ranar 30 ga watan Junairu.
Shugaban kasar ta hannun mataimakinsa Kashim Shettima ya bukaci kwamitin da ya gabatar da rahotonsa ga majalisar zartarwar kasar kafin ranar 1 ga watan Afrelu.
Asali: Legit.ng