Halin Kunci: 'Yan Sanda da Hukumar NEMA Sun Dauki Mataki Yayin da Ake Kai Farmaki Rumbunan Abinci

Halin Kunci: 'Yan Sanda da Hukumar NEMA Sun Dauki Mataki Yayin da Ake Kai Farmaki Rumbunan Abinci

  • Yayin da ake cikin wani mawuyacin hali a Najeriya, fashe-fashen rumbunan kayan abinci sai karuwa suke yi a kasar
  • Dalilin haka, rundunar ‘yan sanda a Legas ta baza jami’anta zuwa ma’ajiyar abinci da manyan kantuna a jihar
  • Har ila yau, Hukumar ba da agaji ta NEMA ta tsaurara tsaro a wuraren da take ajiyar kayan abinci a yankin Kudu maso Yamma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas – Rundunar ‘yan sanda a Legas ta tsaurara tsaro a ma’jiyar abinci ta gwamnati da kuma manyan kantuna saboda gudun kai hari na bata gari.

Rundunar ta dauki matakin ne yayin da wasu jihohi ke fuskantar barazanar fasa wuraren ajiyar abinci yayin da ake cikin wani hali.

Kara karanta wannan

Shugaban Miyetti Allah ya shiga hannun jami'an tsaro, an bayyana matakin gaba

Yan sanda da hukumar NEMA sun tsaurara tsaro game da masu fasa rumbun a abinci
Yan sanda a Legas sun baza jami'an tsaro domin dakile fashin rumbun abinci. Hoto: NEMA, Lagos Police Command.
Asali: Facebook

Wane mataki aka dauka a Legas?

Har ila yau, Hukumar ba da agaji ta NEMA ta tsaurara tsaro a wuraren da take ajiyar kayan abinci a yankin, cewar Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwamishinar ‘yan sanda a jihar Legas, Adegoke Fayoade ta ce sun baza jami'an ‘yan sanda masu farin kaya don kula da wuraren.

Fayoade ta umarci dukkan DPO da ke jihar su zauna a shirin ko ta kwana domin dakile faruwar harin a fadin jihar baki daya.

Martanin kakakin 'yan sanda a Legas

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin shi ya bayyana haka ga manema labarai ta wayar tarho.

Hundeyin ya ce rundunar ta himmatu wurin tabbatar da tsare lafiya da kuma kare dukiyoyin al’umma a jihar, rahoton Nigerian Bulletin.

Ya ce duk da rundunar basu tsammanin harin amma baza jami’an tsaro ya zama dole domin dakile faruwar hakan a jihar.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga da tawagarsa ta addabi jihar Katsina

Mariya ta yi magana kan fashin rumbun abinci

A baya, mun ruwaito muku cewa Ministar Abuja, Dakta Mariya Mahmoud ta yi martani kan fashin rumbun abinci a Abuja.

Mariya ta ce wannan sata ce tsantsarta da matasan suka saba yi ba wai maganar yunwa da ake fama da ita ba ce.

Wannan martani nata na zuwa ne bayan wasu bata gari sun kai farmaki rumbun abuinci tare da satar kayan abinci da sauran abubuwa masu amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.