Talaka Ya Kusa Daina Kukan Wahalar Fetur, Yan Kasuwa Za Su Fara Sayar da Gas Ɗin CNG

Talaka Ya Kusa Daina Kukan Wahalar Fetur, Yan Kasuwa Za Su Fara Sayar da Gas Ɗin CNG

  • Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN ) ta ce tana tattaunawa da gwamnatin tarayya domin fara sayar da gas din CNG a fadin Najeriya
  • IPMAN, ta bakin mataimakin shugabanta na kasa, Hammed Fashola, ta ce za suyi amfani da gidajen mai wajen sayar da gas din
  • Kungiyar na fatan wannan matakin zai taimaka wajen kawo karshen wahala da tsadar man fetur da 'yan Najeriya ke fama da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya ta bayyana cewa tana tattaunawa da gwamnatin tarayya domin fara sayar da gas din CNG.

Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN na kasa, Hammed Fashola, ya tabbatar da hakan a wata tattaunawa ta musamman da jaridar Punch a ranar Talata.

Kara karanta wannan

Ramadan: Sanatan Arewa na shirin rabawa mutanen jiharsa tirelolin abinci 358

Gwamnati ta kaddamar da motocin CNG
Wadatuwar gas din CNG zai rage wahalar man fetur, in ji IPMAN. Hoto: Presidency Nigeria, Pikke (Getty Images)
Asali: Getty Images

Fashola, ya ce za su yi amfani da gidajen man da su ke da su a fadin kasar wajen sayar da gas din CNG domin gaggauta wadatar da shi a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan cire tallafin man fetur, gwamnatin tarayya na ta kokarin saka hannun jari a iskar gas a matsayin mafi araha da tsafta maimakon man fetur da dizal.

IPMAN ke da kaso 80 na gidajen mai a Najeriya

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakin gina gidajen sayar da iskar gas guda 9,000 domin wadatuwar gas din a matakin janye wa daga yawan amfani da fetur.

Ya kuma yi nuni da cewa ‘yan kasuwar sun gana da gwamnatin tarayya domin gyara hanyoyin samar da gas din a fadin Najeriya.

Mambobin kungiyar IPMAN ne ke da mallakin sama da kaso 80 cikin 100 na gidajen mai a lungu da sako na kasar nan.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Yadda IPMAN ta shirya sayar da CNG

Ya ce za su samar da wurin sauya manyan motoci daga amfani da dizal zuwa gas din CNG, yayin da kuma za su samar da kayayyakin tabbatar da hakan.

“Idan muna da CNG, zai maye gurbin man fetur da dizal ne. Zai yi arha, kuma mutane za su sami zabi ba wai lallai sai su dogara da fetur ba."

- A cewar Fashola.

Fashola, ya kuma ce ‘yan kungiyar IPMAN suna son sayar da CNG da kayan hada shi kamar yadda a halin yanzu suke sayar da man fetur a gidajen mai.

Dan Najeriya ya mayar da motarsa zuwa CNG

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito wani dan Najeriya, ya wallafa bidiyon yadda ya sauya motarsa ta koma amfani da gas din CNG sakamakon tsadar da fetur ya yi.

Ya bayyana cewa, ya kashe naira 60,000 wajen sauya injin motar daga amfani da fetur zuwa amfani da gas din CNG, kuma naira 1,800 ke cika tankin motar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.