Mun Hakura: Kungiyar IPMAN Ta Fasa Rufe Gidaje Mai, Tace Mambobi Su Bude

Mun Hakura: Kungiyar IPMAN Ta Fasa Rufe Gidaje Mai, Tace Mambobi Su Bude

  • Bayan barazanar tafiya yajin aiki sai baba ta gani, kungiyar IPMAN ta ce yanzu ta hakura
  • Mambobin IPMAN sunce yan kasuwan mai masu sayan man daga hannun kamfanin man gwamnati NNPC
  • Kimanin watanni biyar kenan yan Najeriya na fama da tsadar man fetur a fadin tarayya

Borno - Kungiyar yan kasuwan mai masu zaman kansu, IPMAN, shiyyar jihar Borno ta janye umurnin rufe dukkan gidajen mai a fadin jihar da tayi jiya.

IPMAN tace yanzu dukkansu su bude yanzu.

Shugaban IPMAN na jihar, Mohammed Kuluwu, ya bayyana hakan ranar Talata.

Wannan ya biyo bayan umurnin rufe dukkan gidajen man mambobinsu a jihar saboda kokarin wajabta musu sayar da litan mai kasa da N195.

A sabon jawabin da IPMAN ta fitar, tace:

"Bayan tattaunawa da hukuma, muna umurnin a bude dukkan gidajen mai kuma a cigaba da sayar da man fetur yayinda kungiyar ke cigaba da tattaunawa kuma zamu sanar da ku yadda akayi."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban INEC Ya Sa Labule Da Gwamnan CBN Saboda Karancin Takardun Naira

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ipman
Mun Hakura: Kungiyar IPMAN Ta Fasa Rufe Gidaje Mai, Tace Mambobi Su Bude hoto: @Leadership
Asali: Twitter

Kakakin IPMAN ya tabbatar

Kakakin kungiyar, AbdulKadir Mustapha, ya tabbatar da wannan sabon umurni da akayi.

A hirarsa da Premium Times, ya bayyana cewa:

"Hakane, maganar dakatar da sayar da mai gaskiya ne amma mun yi sulhu kuma mun umurci dukkan mambobinsu su bude gidajen mansu."

Abinda ya haddasa sabani

A ranar Litinin, IPMAN ta roki gwamnatin tarayya ta basu karin lokaci su gama sayar da man feturin dake gidajen mansu a farashin N195 ga lita.

Mataimakin shugaban IPMAN na shiyyar yammacin Najeriya, Joseph Akanni, hukuma ta tilasta sayar da feturinsu a farashin N195 ga Lita a dadin tarayya.

A cewarsa:

"Tuni mun umurci mambobinmu kada su sayi fetur mai tsada. Hannun NNPC kadau zamu sayi mai."
"Hakazalika mun baiwa mambobinmu shawara kada su sayi feturin da ba zasu iya sayarwa N195 ba kamar yadda gwamnatin tarayya tayi umurni."

Kara karanta wannan

"Nima Ina Ji A Jiki Na", Minista Mai Karfi A Gwamnatin Buhari Ya Ce Shi Kansa Ba Shi Da Sabbin Takardun Naira

"Mun roki hukuma ta samu lokacin gama sayar da sauran feturinmu, wannan shine gaskiya magana saboda masu cewa mambobinmu sun fusata."

Asali: Legit.ng

Online view pixel