Kakakin Majalisar Bauchi da Mataimakinsa Sun Yi Murabus, an Samu Cikakken Bayani
- Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi Babayo Akuyam da mataimakinsa Ahmed Abdullahi sun yi murabus daga mukamansu
- Wannan na zuwa ne bayan da tsohon shugaban majalisar, Abubakar Suleiman da mataimakinsa Jamilu Dahiru suka dawo majalisar
- A watan Nuwamba, 2023 kotu ta kwace kujerun Suleiman da Dahiru, amma suka sake dawo wa majalisar bayan lashe zabe karo na biyu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Bauchi- Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Babayo Akuyam da mataimakinsa Ahmed Abdullahi sun yi murabus daga mukamansu.
Mista Akuyam (PDP – Hardawa), da kuma Abdullahi (PDP – Dass) sun sanar da murabus dinsu a zauren majalisar a ranar Laraba.
Sun yi murabus din ne domin share fagen komawar tsohon shugaban majalisar, Abubakar Suleiman da mataimakinsa, Jamilu Dahiru kan mukamansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Suleiman da Dahiru sun sake lashe zabe
Premium Times ta ruwaito cewa Kotun Daukaka Kara, a watan Nuwamba 2023, ta kwace kujerun Mista Sulaiman (PDP- Ningi ta tsakiya), da Mista Dahiru (PDP – Bauchi ta tsakiya).
Kotun ta kuma ba hukumar zabe tasa (INEC) umarni da ta sake gudanar da zabe a mazabunsu a ranar 11 ga Maris 2023.
Sai dai hukumar INEC, ta bayyana Suleiman da Dahiru a matsayin wadanda suka lashe zaben da aka sake gudanarwa a ranakun 3 ga watan Fabrairu da 4 ga watan Fabrairu.
Yarjejeniyar dawo da majalisa hannun Suleiman
Kakakin majalisar mai barin gado, Mista Akuyam, ya ce matakin na daga cikin yarjejeniyar da ‘yan majalisar suka amince da su na yin murabus domin baiwa tsofaffin shugabannin damar komawa kan mukamansu.
Ya godewa ‘yan majalisar da ma’aikatan majalisar bisa goyon bayan da suka ba su a lokacin tafiyar da harkokin majalisar.
Tribune Online ta ruwaito Mista Suleiman ya na yabawa shugaban majalisar mai barin gado da mataimakinsa bisa yadda suka kiyaye alkawarin.
Ya kuma yi alkawarin samar da dokoki masu inganci domin inganta rayuwar al’umma.
Yan majalisar Bauchi sun zabi kakaki da mataimaki
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa, 'yan majalisa a Bauchi sun zabi Babayo Akuyam a matsayin kakakin majalisa, tare da Ahmed Abdullahi matsayin mataimakinsa.
Zaben Akuyam da Abdullahi na zuwa ne bayan da Kotun Daukaka Kara ta tsige kakakin majalisar mai ci, Abubakar Suleiman da mataimakinsa Jamilu Dahiru.
Kotun ta ce ta tsige Suleiman da Dahiru ne saboda zaben mazabunsu na cike da kura-kurai, tare da ba hukumar INEC damar gudanar da wani zaben.
Asali: Legit.ng