Tsadar Rayuwa: 'Yan Majalisa Sun Ba Tinubu Shawara Kan Albashin da Ya Kamata a Biya Ma'aikata

Tsadar Rayuwa: 'Yan Majalisa Sun Ba Tinubu Shawara Kan Albashin da Ya Kamata a Biya Ma'aikata

  • Ƴan majalisar wakilai sun buƙaci Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya ƙara albashin ma’aikata yayin da matsalar tattalin arziƙi ke ƙara tsananta
  • Yayin da take bayyana damuwarta kan hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, majalisar wakilai ta yi kira da a biya ma’aikatan Najeriya albashin N100,000
  • Ƴan majalisar a ranar Laraba, yayin zaman majalisar sun yi nuni da cewa, babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa a Najeriya da albashi ƙasa da N100,000 duk wata a yanzu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Yayin da hauhawar farashin kayayyaki ke ƙara tsananta, a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, majalisar wakilai ta yi kira da a biya ma’aikatan Najeriya albashi mai kyau.

Jaridar Daily Trust ta ce majalisar ta kuma umarci kwamitocin kwadago da samar da ayyuka, kuɗi da tsare-tsare da su tsara hanyoyin biyan albashin ma’aikatan Najeriya a farashin da ya yi daidai da yanayin tattalin arziƙin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

'Yan majalisa sun ba Tinubu shawara
Majalisar wakilai na son Tinubu ya ba ma'aikata albashi mai kyau Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Wannan matakin ya biyo bayan amincewa da wani ƙudirin da ƴan majalisa 40 suka ɗauki nauyi, inji rahoton Daily Independent.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa majalisa ke son a ba ma'aikata albashi mai kyau?

Da yake jagorantar muhawara kan ƙudirin, mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar, Aliyu Madaki, ya ce hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya sa talakawan Najeriya cikin wahala.

Ya yi nuni da cewa biyan buƙatun yau da kullum da suka haɗa da abinci, ruwa, gidaje, ilimi, kiwon lafiya, sufuri, tufafi, da sauransu na neman gagarar ƴan Najeriya.

A cewarsa:

"Hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar nan ya yi mummunan tasiri a kan tsadar rayuwa, inda farashin abinci, wurin kwana, ilimi, da sufuri ya yi tashin gwauron zabi."

Duba da yanayin tattalin arziƙin da ƙasar nan ke ciki, majalisar ta yi nuni da cewa babu wani ma’aikaci da zai iya rayuwa a Najeriya da albashi ƙasa da N100,000 a kowane wata.

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

Tinubu Ya Umarci a Raba Abinci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi umarnin da a gaggauta raba wa mazauna birnin tarayya kayan hatsi da abinci.

Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin ne ga ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, domin rage raɗaɗin halin da mutane ke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng