Shugabannin Majalisa Za Su Gana da Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Fito
- Majalisar dattawa ta yanke shawarar shugabannin majalisar tarayya za su gana da Shugaba Bola Tinubu kan matsalar rashin tsaro
- Majalisar ta amince da hakan ne bayan an gabatar da wani ƙudiri a gabanta wanda ya bayyana ta'asar da ƴan ta'adda suka tafka a wasu ƙauyukan jihar Benuwai
- Majalisar za ta kuma tura wata tawaga domin ta'aziyya ga gwamnati da al'ummar jihar Benuwai kan kashe-kashen da aka yi a jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A ranar Laraba majalisar dattawa ta yanke shawarar cewa shugabannin majalisar tarayya za su gana da shugaban ƙasa Bola Tinubu kan ƙalubalen tsaro a ƙasar nan.
Hakan dai ya biyo bayan wani ƙudirin da Sanata Emmanuel Udende ya gabatar kan kashe mutane sama da 50 a sababbin hare-haren da ƴan ta’adda suka kai a wasu ƙauyuka guda biyar na jihar Benue, cewar rahoton Channels tv.
Ƙudirin ya kuma yi magana kan rashin tsaro da ake fama da shi a ƙananan hukumomin Kwande, Ukum, Logo da Katsina-Ala na jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bisa ƙudirin, majalisar dattawan ta kuma ƙuduri aniyar tura tawaga domin ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar jihar Benuwai.
Majalisa ta ba hukumomin tsaro sabon umarni
Ƴan majalisar sun kuma buƙaci hafsan hafsoshin tsaro, hafsan sojin ƙasa, hafsan sojan sama, Sufeto Janar na ƴan sanda da shugabannin sauran hukumomin tsaro da su gaggauta tura jami’an tsaro domin magance matsalar tsaro a yankin.
A cewar majalisar, hakan zai taimaka wajen dakatar da kashe-kashen, da kuma dawo da zaman lafiya a cikin ƙauyukan da abin ya shafa.
Majalisar dattawan ta kuma buƙaci manyan hafsoshin tsaro da IGP su ƙara sa ido da kuma sayo kayayyakin leƙen asiri don ganowa da hana kai hare-hare nan gaba.
Jihar Benuwai dai ta daɗe tana fuskantar hare-hare ƴan ta'adda, inda mutane da dama suka rasa rayukansu sakamakon tashin hankalin.
A cikin watanni uku da suka gabata, an yi garkuwa da shugaban ƙaramar hukumar Ukum, Rabaran Gideon Haanongon, da kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar, Matthew Abo.
Majalisa Ta Umurci a Ɗauki Ƴan Sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar dattawa ta bada umurnin a ɗauki jami'an ƴan sanda 10 a cikin kowace ƙaramar hukuma da ke Najeriya.
Majalisar ta bayar da wannan umurnin ne ga hukumar kula da jindaɗin ƴan sannda da hukumar ƴan sandan don bunƙaso ayyukan tsaro.
Asali: Legit.ng