Da Gaske an Samu Bullar Muguwar Cuta a Jihar Kano? Gwamnati Ta Fayyace Gaskiya

Da Gaske an Samu Bullar Muguwar Cuta a Jihar Kano? Gwamnati Ta Fayyace Gaskiya

  • Gwamnatin jihar Kano ta karyata rahoton bullar cutar kyanda a karamar hukumar Kano, babban birnin jihar
  • Dakta Imam Wada Bello, daraktan kula da lafiya da yaki da cututtuka na ma'aikatar lafiya ta jihar ne ya karyata rahoton
  • Dakta Imam ya ce wadanda suka fitar da rahoton bullar cutar ba su bi matakai da gwaje-gwaje da ya kamata a aiwatar ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta musanta rahoton bullar cutar kyanda a karamar hukumar Kano, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da sashin hulda da jama’a na ma’aikatar ya fitar, ya ruwaito daraktan kula da lafiya da yaki da cututtuka, Dakta Imam Wada Bello ya karyata bullar cutar.

Kara karanta wannan

BUK ta ba Abba Yusuf lambar yabo yayin da ilimi ya samu 30% a kasafin Kano a 2024

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnati ta ce cutar 'kyanda' ba ta bulla a Kano ba. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Dakta Imam ya karyata bullar cutar kyanda a Kano

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa hukumomi a karamar hukumar Kano ta sun tabbatar da bullar cutar kyanda a wasu sassan karamar hukumar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kula da lafiya a matakin farko na yankin, Aliyu Jinjiri Kiru, ya bayyana haka a lokacin wani taro na kwamitin bayar da agajin gaggawa a sakatariyar karamar hukumar.

Amma jaridar Daily Trust a ranar Laraba, ta ruwaito Dakta Imam na karyata bullar cutar, inda ya yi nuni da cewa, akwai matakai da gwaje-gwaje da ya kamata a aiwatar kafin yanke hukunci.

Matakan kariya da ma'aikatar ta dauka a Kano

Dangane da lamarin na karamar hukumar Kano, a cewarsa:

“Babu daya daga cikin hanyoyin ko matakan gwaji da aka bi wajen tabbatar da bullar cutar kyandar, wanda ya zama wajibi ga jama’a suyi watsi da rahoton."

Kara karanta wannan

Shugaban Miyetti Allah ya shiga hannun jami'an tsaro, an bayyana matakin gaba

Daraktan ya ce ma’aikatar na taka-tsan-tsan da duk wata cuta da ta shafi al’umma ta hanyar daukar matakan da suka dace domin dakile bulla ko yaduwar irin wadannan cututtuka.

Ya kuma ba da tabbacin cewa, a shirye ma’aikatar tare da jami'anta na ba da agajin gaggawa (EPR) da ke a kananan hukumomi 44 na jihar su ke kullum don dakile barkewar annoba.

Nazari domin gano inda matsalar ta samo asali

Da aka tuntubi jami’in kula da lafiya a matakin farko na karamar hukumar Kano, Aliyu Jinjiri Kiru, wanda aka alakanta rahoton bullar cutar da shi, ya ce ko kadan bai sanar da hakan ba.

Ya kuma jaddada cewa sashen yada labarai na karamar hukumar ya yi amfani da wani rahoto na taron EPR bisa kuskuren fahimta a wajen fitar da sanarwar bullar cutar.

Kiru ya ce, abin da rahoton da hukumar ta bayar shi ne, ta samu "rahoton bullar cutar kyanda da maƙogwaro” daga cibiyoyin kiwon lafiya a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya yi muhimman nade-nade a kananan hukumomin jiharsa

Kano: Gwamna ya nada kantomomin riko

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nada kantomomin riko na kananan hukumomin jihar 44, gabanin gudanar da zabe.

Gwamnan ya aike wa majalisar jihar sunayen kwamitin mutum 14 da za su jagoranci mulkin kowacce karamar hukumar domin tantancewa.

Hakazalika, gwamnan ya aikewa majalisar sunayen mutum 7 da ya ke so a nada kwamishinoni a hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.