Covid-19: Hotunan cibiyar killace masu jinyar cutuka masu yaduwa a Kano
- A yayin da annobar cutar coronavirus ta barke a kasashen duniya, Najeriya ta shiga sahun kasashen da ke fama da cutar
- Legas ce jiha ta farko a kasar nan da aka samu mai dauke da muguwar cutar. Babu kakkautawa kuma cikin gaggawa gwamnatin jihar ta gyara cibiyar killace masu jinyar cutuka masu yaduwa
- A yayin da sauran jihohi ke faman gyara tare da inganta cibiyoyin lafiya, wasu jihohin sun kalmashe kafa tare da jira har sai cutar ta iso jihar kafin su yi abinda ya dace
A yayin da annobar cutar coronavirus ta barke a kasashen duniya, Najeriya ta shiga sahun kasashen da ke fama da barkewar cutar. Amma kuma babban abun tsoro shine yadda cibiyoyin kiwon lafiyar kasar nan suke.
Legas ce jiha ta farko a kasar nan da aka samu mai dauke da muguwar cutar. Babu kakkautawa kuma cikin gaggawa gwamnatin jihar ta gyara cibiyar killace masu jinyar cutuka masu yaduwa da ke Yaba a jihar.
A yayin da sauran jihohi ke fama gyara tare da inganta cibiyoyin lafiya da kuma na killace masu jinya cuwuka masu yaduwa, wasu jihohin sun kalmashe kafa tare da jira har sai cutar ta iso jihar kafin su yi abinda ya dace.
A lokacin da jaridar The Cable ta kai ziyara cibiyar killace masu jinyar cuwuka masu yaduwa da ke Yar Gaya a karamar hukumar Dawakin Kudu ta Kano, tabarbarewa da lalacewar ginin abun mamaki ne.
Ga wasu daga cikin hotunan cibiyar:
KU KARANTA: Abinda ya hana Abba Kyari killace kansa bayan dawowa da kasar Jamus
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng