Tsadar Rayuwa: Fitaccen Basarake Ya Tura Sako Ga Tinubu Kan Kafa Hukumar Kayyade Farashi
- Oba na Iwoland, Abdulrosheed Akanbi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya samar da hukumar kayyade farashin kaya a kasar
- Akanbi ya ce wannan mataki ne kadai zai dakile hauhawan farashin da wasu masu hadama ke yi a duk lokacin da suka ga dama
- Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Mista Alli Ibraheem ya fitar a yau Laraba 6 ga watan Maris
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Fitaccen basarake a Najeriya, Oba na Iwoland, Abdulrosheed Adewale Akanbi ya shawarci Shugaba kan dakile tsadar kayayyaki.
Mai Martaban ya ce bukaci Tinubu ya kafa hukumar kayyade farashin kaya don kawo karshen matsalolin da ake ciki.
Wace shawara Sarki Akanbi ya bai wa Tinubu?
Akanbi ya ce hakan ne kadai zai dakile masu kayayyaki da suke da hadama da sauran ‘yan kasuwa da ke kara farashin kaya, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bukaci shugaban da ya yi gaggawar daukar matakan da za su tabbatar da an samu sauki ga ‘yan kasar da ke cikin wani hali.
Sarkin ya bayyana haka ne ta bakin sakataren yada labaransa, Mista Alli Ibraheem inda ya ce kayyade farashin zai kare hakkin masu siyan kayan.
Ya yabawa Tinubu kan tsare-tsarensa
Ya yi Allah wadai ganin yadda kullum farashin ke karuwa inda ya ce wasu da gan-gan suke kara kudin kayan a karan kansu.
“Idan har karin farashin kaya da ake fuskanta gwamnati ba ta dauki mataki a kai ba to tabbas Najeriyaza ta ci gaba da durkushewa."
- Adewale Akanbi
Ya ce tabbas Tinubu mutum ne mai kwanya da son ci gaban kasa inda ya ce akwai sa ran shugaban zai kawo karshen matsalolin tattalin arziki da ake ciki, cewar Tribune.
Moghalu ya tsokaci kan halin da ake ciki
Kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan CBN, Farfesa Kingsley Moghalu ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a Najeriya.
Moghalu ya ce tabbas halin da ake ciki a yanzu sai an shafe shekaru uku zuwa biyar saboda yadda aka birkita tattalin arziki.
Wannan martani na Moghalu na zuwa ne yayin da ake cikin matsin tattalin arziki da tsadar kayayyaki.
Asali: Legit.ng