An Shiga Jimami Yayin da Dalibi Ya Rasa Ransa a Abuja, An Fadi Dalilin Mutuwar

An Shiga Jimami Yayin da Dalibi Ya Rasa Ransa a Abuja, An Fadi Dalilin Mutuwar

  • An shiga jimami a babban birnin tarayya Abuja, bayan da wani ɗalibin makarantar sakandire ya rasa ransa
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ɗalibin ya rasu ne bayan ya taka wayar wutar lantarkin da ta faɗo a harabar makarantar
  • Rundunar ƴan sandan birnin tararayya Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce tana ci gaba ɗa gudanar da bincike

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Wani iftila'i ya afku a makarantar sakandiren gwamnati da ke Maitama a babban birnin tarayya Abuja, yayin da wani ɗalibi ya rasa ransa.

Jaridar The Punch tace ɗalibin mai suna Meshack Agaba, mai shekara 16 a duniya ya rasu ne sakamakon taka wayar wutar lantarki a harabar makarantar.

Kara karanta wannan

Dangote, Otedola da Minista za su bunkasa makarantun koyon aikin shari'a na Najeriya

Dalibi ya rasu a Abuja
Dalibin sakandire ya rasa ransa a Abuja Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Jaridar ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar da ta gabata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda lamarin ya auku

Wani daga cikin iyayen ɗalibai wanda ke da masaniya kan lamarin amma ya nemi sakaya sunansa, ya ce ɗalibin ya rasu ne lokacin da yake kan hanyar zuwa ɗebo ruwa daga famfo.

Ya bayyana cewa ya taka wayar wutar lantarki ce da ta faɗo daga jikin wata falwayar da ta lalace a harabar makarantar, rahoton The Street Journal ya tabbatar.

A kalamansa:

"Ɗakin kwanansu ɗaya da yarona. Wurin ya yi santsi da yawa yayin da yake ƙoƙarin wucewa kawai sai ya zame cikin tsautsayi ya taka wayar wutar lantarkin.
"Na yi mamakin cewa ko bayan faruwar lamarin, mahukuntan makarantar ba su gyara wannan falwayar ba. Abin da kawai suka yi shi ne sanya hoton yaron a bango tare da rubutun 'ka yi saurin tafiya'."

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan shugaban jam'iyyar APC ya riga mu gidan gaskiya

Iyayen yaron sun koka da cewa mahukuntan makarantar sun yi ta ƙoƙarin sauya labarin bayan da ƴan sanda suka shiga lamarin, inda suke cewa ya je tsallaka kataga ne wayar ta faɗo masa.

Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?

Sai dai, jami'ar hulɗa da jama’a ta rundunar ƴan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin a lokacin da aka tuntuɓe ta.

Ta bayyana cewa tuni rundunar ta fara bincike kan lamarin.

An Ɗauke Wuta a Majalisa

A wani labarin kuma, kun ji cewa zaman majalisar dattawa ya samu tsaiko bayan da aka ɗauke wutar lantarki na wani lokaci.

Ɗauke wutar lantarkin dai ta tilasta sanatocin zaman jiran dawowarta kafin su fara zaman majalisar na ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng