Ga Sarauta Ga Kudi: Muhammadu Sanusi II Na Shirin Zama Surukin 'Dan Siyasar Kwara

Ga Sarauta Ga Kudi: Muhammadu Sanusi II Na Shirin Zama Surukin 'Dan Siyasar Kwara

  • Diyar tsohon sarkin Kano Muhammad Sanusi 11, Yusrah za ta shiga daga ciki da hadadden angonta, Abdulmutallib Akintade Shittu
  • Za a daura auren Gimbiya Yusrah da sahibin nata wanda ya kasance Bayarabe a ranar Juma'a, 19 ga watan Afrilu, a garin Kano
  • Akintade Shittu wanda ya fito daga Kwara shi ne Shugaban hukumar tattara bayanan kasa (GIS) na jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Gimbiya Khadija Yusrah, diyar tsohon sarkin Kano kuma Khalifan darikar Tijjaniyah a Najeriya, Muhammad Sanusi II za ta shiga daga ciki.

Za a daura auren Yusrah da angonta mai suna Abdulmutallib Akintade Shittu a ranar Juma'a, 19 ga watan Afrilu, a jihar Kano.

Yusrah Sanusi za ta amarce da Shittu
Yusrah Sanusi za ta auri Mutallib Shitu a Kano Hoto: fashionseriesng
Asali: Instagram

Kamar yadda shafin fashionseriesng ya wallafa a Instagram, za a daura auren masoyan ne a mahaifar amarya.

Kara karanta wannan

Kannywood-Nollywood: Mista Ibu da fitattun jarumai 4 da suka mutu a shekarar 2024

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akintade Shtittu ya kasance Bayarabe kuma Shugaban hukumar tattara bayanan kasa (GIS) na jihar Kwara.

Ga hotunan masoyan a kasa:

Jama'a sun yi martani kan auren 'diyar Sanusi II

cute_fiyyah ta yi martani:

"Ita kuma Bayarabe ta samo ikon Allah Allah Ya sanya alkhairi."

zainabaliyubabayo ta ce:

"Abun burgewa irin wanna abin na burgeni sosai Yarbawa suna da kirki gaskiya."

maamah94 ta ce:

"Ai garama yarabawan ba saki wlh aeta hkr kuma akwai dadi wlh."

saif_made ta yi martani:

"Auren yarbawa fa babu saki kin yi daidai 'yar sarki "

maaiman_catering ta yi martani:

"Allah ya sanya alkhairi ya kade fitina Ameen."

abaya_souk_by_deejah ta ce:

"Kwarai kuwa 'dan uwana daga offa Allah ya albakaci auren."

yasminnamada ta ce:

"Tabarakallahu maa sha Allah."

ohmar_gaddaf:

"Suna ma kama, toh Amin ya Allah "

Kakakin 'yan sandan Gombe ya angwance

Kara karanta wannan

Za a dauke wasu na'urori daga Kwalejin Zaria zuwa Legas? Gaskiya ta fito bayan zargin Dattawan Arewa

A wani labarin kuma, kakakin 'yan sandan jihar Gombe, Mahid Abubakar, ya angwance da kyakkyawar amaryarsa mai suna Nafisa a ranar Asabar, 24 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma, labarin soyayyarsu da jami'in 'dan sandan ya bayar a shafinsa na X a ranar Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, shine babban abin da ya dauki hankalin jama'a.

Matashin 'dan sandan ya bayyana cewa ya fara yin arba da Nafisa a 2010, sai dai kuma bai fallasa mata sirrin zuciyarsa ba saboda karancin shekarunta a wancan lokacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel