Yadda wani Mutumi ya rika kwana da ‘yar karamar Yarinya
Dama an ce abin Duniya da yawa yake. Kwanan nan mu ka ji labari wani Mutumi da yayi gaba da wata ‘Yar karamar Yarinya mai shekaru 12 zuwa wajen kwanan sa inda kuma yace ta san shi. Har sai da ta kai an kai kara wajen Hukuma.
Wani Mutumi ne mai shekaru da dama ake shari’a da shi yanzu haka a Garin Kubwa da ke Babban Birnin Tarayya Abuja da ake zargi ya rika kwanciya da wata Karamar Yarinya da duka-duka ba ta wuce shekaru 12 rak a Duniya ba.
Wannan mutumi ya bayyanawa Kotu da bakin sa cewa Yarinyar ta zo wajen sa ne domin bayyana masa cewa Iyayen ta sun yi tafiya. A dalilin haka kuwa ta zauna wajen san a kwanaki kadan. A nan ne fa ya rika tarawa da wannan ‘yar yarinya.
KU KARANTA: Wani Bawan Allah ya kai karar Iyalin sa gaban Alkali
Alkali Mohammed Marafa ya nemi a tsare wannan mutumi mai suna Abubakar a wajen ‘Yan Sanda inda ya daga karar na ‘dan lokaci. Lauyan da ke kare Yarinyar dai yace wannan mutumi ya yaudare ta ne ya rika kwana da ita a gidan sa.
Kwanciya da karamar yarinya irin wannan dai ya sabawa dokar kasa. Shi dai Lauyan da ke kare Abubakar ya nemi rangwamen shari’a wajen Alkali inda yace akwai sakacin Iyayen wanna yarinya da su ka kyale ta a Gari su kayi tafiya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng