“Ku Dauke Kudinku”: Binance Ya Dakatar da Hada Hadar Naira, Ya Aika Sako Ga ’Yan Najeriya
- Babban kamfanin cinikayyar cryptocurrency na duniya, Binance ya dakatar da hada-hadar kudi da ta shafi Naira daga dandalinsa
- Kamfanin zai cire duk wacu kudade ko sulalla da ake hada-hadarsu da NGN daga ranar 7 ga watan Maris 7, kamar yadda sanarwar ta tabbatar
- Masani a harkar Cryptocurrency, Nura Haruna Maikarfe, ya ce matakin da Binance ya dauka ba shi zai hana yin crypto a kasar ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Babban kamfanin cinikayyar cryptocurrency na duniya Binance zai fice daga kasuwar Najeriya, yana mai sanar da dakatar da duk wasu hada-hadar kudi da ta shafi Naira.
Kamfanin ya shawarci abokan huldarsa da ke a Najeriya da su kwashe kudadensu na Naira, ko su sayi wani sulallan daban, ko kuma su juyar da Nairar zuwa dala.
Binance, Naira da Najeriya
"A lura da cewa, darajar sauya NGN zuwa USDT zai ta'allaka ne a kan matsakaicin farashin da aka rufe cinikayyar kudaden biyu a kasuwar 'Binance Spot' cikin kwanaki bakwai da suka gabata ,"
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a shafinsa na yanar gizo.
Binance ta kuma sanar dakatar da saka hannun jari na Naira (NGN), saboda daina amfani da kudin da za ta yi bayan 2:00 na rana UTC a ranar 5 ga Maris.
Kamfanin zai cire duk wasu kudade ko sulalla da ake hada-hadarsu da NGN daga ranar 7 ga watan Maris 7, kamar yadda sanarwar ta tabbatar.
Gwamnatin Najeriya na tuhumar Binance
Hakazalika, kamfanin zai cire NGN daga jerin zababbun hanyoyin biyan kudi na 'Binance Pay' a ranar 6 ga Maris.
Tribune Online ta ruwaito cewa hukumomin Najeriya sun fara gudanar da bincike a kan kamfanin na Binance wanda ya ke aiki a kasar ba tare da izini ba.
A ranar 27 ga watan Fabrairu, gwamnan babban bankin Najeriya ya bayar da hujjar cewa ana zargin Binance na taimakawa wajen gudanar da haramtattun hada-hadar kudin kasar.
Tafiyar Binance ba zai hana crypto ba
Da Legit Hausa ta samu jin ta bakin Nura Haruna Maikarfe, wani matashi wanda ke kasuwancin crypto, ya ce matakin da Binance ta dauka ba zai hana canjin Naira a crypto ba.
Ya ce akwai sauran manhajoji da 'yan Najeriya za su iya amfani da su wajen canja Naira zuwa Dala, kamar su Kucoin, Bybite, da sauran su.
"Zan iya cewa Binance ba ta da wani hurumi ko karfi na karya wa ko daga darajar Naira. Binance wani dandali ne da mutane ke hada hada a tsakaninsu, ba wai tsakanin mutum da kamfanin ba.
"Zai fi kyau ace gwamnati ta sake duba manyan dalilin tashin dala, tare da kawo karshen matsalar. Akwai bukatar ta bunkasa fitar da kayayyaki zuwa waje don samun dalar."
A cewar Maikarfe.
Gwamnatin Najeriya ta tsare jami’an Binance
A baya-bayan nan ne Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin Najeriya ta kama tare da tsare wasu manyan jami’an Binance guda biyu a watan Fabrairu.
Ba a tuhumi shugabannin ba a wancan lokacin, amma za su iya fuskantar tuhumar hada-hadar kudade ba bisa ka'ida ba da kaucewa biyan haraji.
Asali: Legit.ng