Dalili 1 da Ya sa Na Hakura Na Koma Shugabancin Hisbah – Daurawa Ya Yi Magana Mai Ratsa Zuciya
- Sheikh Aminu Daurawa, shugaban hukumar Hisbah ta Kano ya tabbatar da komawa kan kujerarsa bayan sabani da ya samu da gwamnatin jihar
- Daurawa ya ce ya hakura ya koma kujerarsa ne bayan gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya roke shi da ya ci gaba da zuwa ofis
- Shehin malamin ya kuma jaddada cewar gwamnatin Kano ta yi alkwarin samawa 'yan Hisbah kayan aiki don su ci gaba da kawar da badala
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Kano - Shugaban hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Daurawa ya tabbatar da komawarsa kan kujerarsa bayan ya sanar da yin murabus a baya.
Daurawa ya tabbatarwa sashin Hausa na BBC cewa hukumar Hisbah za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta na kawar da badala da tabbatar da tarbiya kamar yadda ta saba a jihar Kano.
Gwamna Abba ya ce in koma Hisbah - Daurawa
Shehin malamin ya ce zai cigaba da yin aiki da gwamnatin Abba Kabir Yusuf domin dama tun farko ba ta karbi takardar ajiye aikin da ya gabatar mata ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Har ila yau, malamin ya tabbatar da cewar gwamnan ya roke shi da ya cigaba da zuwa ofis, saboda haka ne ya hakura.
Ya kuma jaddada cewar Abba Gida Gida ya ce zai cigaba da ba hukumar Hisbah cikakken hadin-kai dari bisa dari, tare da sama mata ingantattun kayan aiki don dorawa daga inda suka tsaya.
Maganar shugaban Hisbah, Aminu Daurawa
A hira da ya yi da sashen Hausa na BBC, an ji Shehin malamin yana cewa:
"Aikin da aka fara ne za a cigaba na tsaftace Kano daga ayyukan badala da kuma gyaran tarbiya.
"In shaa Allah mai girma gwamna ya yi alkawari zai samawa Hisbah kayan aiki domin ta cigaba da wannan aiki, kuma zai cigaba da bata tallafi da goyon baya."
- Aminu Daurawa
Ya ci gaba da cewa:
"Dama gwamnati bata karbi takardar ajiye aiki da na kai ba, kuma yanzu an yi hakuri, mai girma gwamna ya roke ni cewa na cigaba da zuwa ofis domin a kau da shaidan din abubuwan da suka faru.
"Kuma In shaa Allahu ya yi alkawarin zai ba Hisbah cikakken hadin kai dari bisa dari."
- Aminu Daurawa
An yi zaman sulhu tsakanin Abba da Daurawa
A baya Legit Hausa ta rahoto cewa Shugabannin hukumar Hisbah ta jihar Kano sun yi zama da Abba Kabir Yusuf a ranar Asabar bayan wasu abubuwan da suka faru.
An rahoto cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar da ajiye aikin shugabancin hukumar wanda hakan sam bai yi wa al’umma dadi ba.
Asali: Legit.ng