Ramadan: Gwamnan Arewa Ya Yiwa Al’ummar Jiharsa Alkawarin Daina Dauke Wuta

Ramadan: Gwamnan Arewa Ya Yiwa Al’ummar Jiharsa Alkawarin Daina Dauke Wuta

  • Gwamnan Kebbi, Nasir Idris, ya kammala shiri tsaf don ganin ya kawo sauki ga al'ummar jiharsa yayin da ake shirin fara azumi
  • Gwamna Idris ya dauki alkwarin samar da wutar lantarki na tsawon awanni 24 a fadin jihar a lokacin watan Ramadana
  • Ya ce tuni suka fara zaman tattauna hakan da shugaban kamfanin rarraba wutar lantarki na Kaduna don cimma hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na Kebbi ya ce gwamnatinsa ta fara wani yunkuri don tabbatar da ganin ta samar da wutar lantarki na awanni 24 a jihar, a lokacin azumin Ramadana.

Mista Idris ya bayyana hakan ne yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai jim kadan bayan duba ayyukan da ke gudana a Birnin Kebbi, a ranar Litinin, 4 ga watan Maris, rahoton Peoples Gazette.

Kara karanta wannan

Sauƙi ya zo yayin da Gwamnatin Tinubu za ta fara rabon kayan abinci kyauta a jihohin Najeriya

Gwamnan Kebbi na shirin inganta wutar lantarki a lokacin Ramadana
Ramadana: Gwamnan Arewa Ya Yiwa Al’ummar Jiharsa Alkawarin Samar da Wuta Na Awanni 24 Hoto: Willy Ibimina Jim-george
Asali: Facebook

Wani tanadin Ramadan gwamnatin Kebbi ta yiwa al'umma?

Ya bayyana cewa tuni ya gayyaci manajan darakta na kamfanin rarraba wutar lantarki ta Kaduna (KAEDCO) domin tattaunawa a kan yadda za a ceto al’ummarsa don su samu wutar lantarki na sa’o’i 24 a cikin watan Ramadana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idris, wanda ya nuna rashin jin dadinsa kan matsalar wutar lantarki da ake fuskanta a fadin jihar, ya nanata cewa yana son ganin an inganta wutar lantarki a Ramadan.

Gwamnan ya ce:

"Tuni na gayyaci Manajan Darakta na KAEDCO domin zama a tattauna kan yadda za mu sanya farin ciki kan fuskokin mutanen jihar masu karamci.
“Burina shi ne in tabbatar da samar da wutar lantarki na tsawon sa’o’i 24, musamman a wannan wata mai alfarma na Ramadana."
"A kan haka, a shirye nake in tallafa wa kamfanin ta kowane bangare don cimma wannan manufa In-Sha-Allah."

Kara karanta wannan

Minista ya dauki zafi, ya kama shirin daukar matakin matsalar wutar lantarki

Gwamnan ya ce yana duba yiwuwar ci gaba samar da wutar lantarkin har zuwa bayan Ramadana.

Za mu cika alkawaran zaben da muka dauka - Gwamna Idris

Ya kuma sha alwashin yin tsayin daka wajen cika dukkan alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe na sauya daukaka jihar, da tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Haka kuma, gwamnan ya yabama dukkanin 'yan kwangilar da ke jagorantar ayyukan da ake gudanarwa a jihar, kan yadda suke gudanar da ayyuka masu kyau da kuma ma’aikatun da ke sanya ido kan ayyukan.

Gwamnan ya yi alkawarin kaddamarwa tare da aiwatar da wasu ayyuka masu inganci wadanda suka shafi rayuwar al’umma kai tsaye, jaridar The Guardian ta ruwaito.

Sarkin Kano ya yi kira ga 'yan kasuwa kafin Ramadan

A wani labarin kuma, mun ji cewa Sarkin Kano, shawarci ƴan kasuwa da su rage tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki.

Alhaji Aminu Bayero ya yi wannan kiran ne ga ƴan kasuwa domin baiwa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauƙi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng