Majalisa Ta Fara Shirin Daukar Kwakkwaran Mataki Kan Shugabannin Binance, Bayanai Sun Fito

Majalisa Ta Fara Shirin Daukar Kwakkwaran Mataki Kan Shugabannin Binance, Bayanai Sun Fito

  • Kwamitin majalisar wakilai kan laifukan da suka shafi kuɗi ya sanar da aniyarsa ta yiwuwar kama shugabannin kamfanin Binance
  • Wannan ya zo ne bayan da shugabannin kamfanin hada-hadar Kirifto suka kasa bayyana a gaban kwamitin don amsa tambayoyi
  • Majalisar a ranar Litinin, 4 ga watan Maris, ta caccaki matakin na Binance, inda ta yi nuni da cewa ba za ta sake yarda kamfanin ya turo wakilai ba kan binciken da ake yi a kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin majalisar wakilai kan laifuffukan da suka shafi kuɗi ya amince da shawartar majalisar ta yi amfani da ikonta ta aike da sammaci da kama shugabannin kamfanin Binance.

Hakan ya biyo bayan gaza bayyana da shugabannin kamfanin suka yi a zaman binciken da kwamitin ya gudanar a ranar Litinin 4 ga watan Maris, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Minista ya dauki zafi, ya kama shirin daukar matakin matsalar wutar lantarki

Majalisa na shirin ba Binance sammaci
An bukaci shugabannin Binance su bayyana a gaban majalisa Hoto: House of Representatives, Federal Republic of Nigeria
Asali: Facebook

Lambar Binance ta fito a majalisar tarayya

Shugaban kwamitin, Honarabul Ginger Obinna Onwusibe, ya ce an shirya shugabannin kamfanin za su gurfana a gabansu domin amsa tambayoyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce tambayoyi sun shafi wani ƙorafi da aka shigar kan ɗaukar nauyin ta'addanci, halasta kuɗin haram, ƙin biyan haraji, da sauran laifukan kuɗi.

Onwusibe ya fusata bisa turo wakilai da kamfanin ya yi domin halartar zaman.

Meyasa kwamitin ke son cafke shugabannin Binance?

Ya ce a zaman da ya gabata an yanke shawarar cewa dole ne shugabannin kamfanin su bayyana da kansu.

Sai dai lauyan da ke wakiltar Binance, Sanata Ihenyen, ya ce daga cikin dalilan da suka sa shugabannin kamfanin ƙin zuwa, akwai cafke wasu shugabanninsu biyu kwanan nan kuma har yanzu suna tsare.

Hon Obinna ya ce:

“Shugabannin Binance ba su a nan. Mun ɗauki matsaya a zamanmu na ƙarshe cewa ba za mu yarda da turo wakilai ba daga Binance kuma wannan matsayar tana nan.

Kara karanta wannan

Rikicin APC ya tsananta yayin da ƴan danda suka harba barkono kan magoya bayan gwamnan Arewa

"Duba da cewa ba shugabannin Binance a nan, muna buƙatar mu ba da shawara ga majalisa ta yi amfani da ikonta don ba da sammacin cafke shugabannin Binance a kawo su gaban wannan kwamiti su amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake yi musu."

Adamu Garba Ya Magantu Kan Binance

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Adamu Garba, ya yi magana kan matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka kan shugabannin Binance.

Adamu ya yi nuni da cewa lokaci ya yi da kamfanin zai fuskanci hukunci kan yadda yake taimakawa wajen lalata tattalin arziƙin ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng