Sarkin Kano Ya Ba 'Yan Kasuwa Muhimmiyar Shawara Kan Watan Azumin Ramadan
- Mai martaba sarkin Kano, ya ji tausayin talakawa kan halin da ake ciki a ƙasar nan yayin da ake dab da fara azumin watan Ramadan
- Alhaji Aminu Ado-Bayero ya yi kira ga ƴan kasuwa da su sauke farashin kayan abinci da sauran kayayyaki domin ƴan Najeriya su samu sauƙi
- Sarkin na masarautar Kano ya kuma yi addu'ar Allah ya ba jama'ar damar ribatuwa da alkhairan da ke cikin watan Ramadan mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero, ya yi kira ga ƴan kasuwa da su rage tsadar kayan abinci da sauran kayayyaki.
Sarkin ya yi wannan kiran ne ga ƴan kasuwa domin baiwa talakawa damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauƙi, cewar rahoton jaridar The Punch.
Sarki Aminu Bayero a wajen kaddamar da littafi
Mai martaban ya buƙaci hakan ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Maris a Zaria lokacin ƙaddamar da wani littafi mai suna “Dauloli a Ƙasar Hausa" na Farfesa Sa’idu-Mohammed Gusau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Farfesa Gusau malamin harshen Hausa ne a jami'ar Bayero da ke Kano, ya yi digirorin BA, MA da PhD a 1980, 1983 da 1989.
Wacce shawara sarkin Kano ya ba masu hannu da shuni?
Aminu Ado-Bayero ya kuma shawarci ƴan Najeriya masu hannu da shuni da su riƙa taimakawa marasa galihu a cikin watan Ramadan, rahoton da jaridar Gazettengr ya tabbatar.
Ya kuma yi addu’ar Allah Ta’ala ya ba al’umma tsawon rai domin su samu ganin watan mai alfarma cikin ƙoshin lafiya da kuma karɓar addu’o’i da sadakokin da za su yi.
Sarkin ya yabawa mawallafin littafin kan yadda yayi bayani dalla-dalla kan masarautun Hausawa a Kano, Katsina, Zamfara, Kebbi, Zazzau da dai sauransu.
A kalamansa:
"Sun bayar da cikakken bayani kan tsarin gudanar da mulki da kowace masarauta ta shimfida, sana’o’insu, ƙa’idoji da ɗabi’unsu."
Sarkin Kano Ya Shawarci Kwastam
A wani labarin kuma, kun ji cewa mai martaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado-Bayero ya buƙaci hukumar hana fasa ƙwauri watau Kwastam, da ta bar ƴan kasuwa su sarara.
Sarkin ya yi wannan kiran ne yayin da hukumar ke.ci gaba da kama motocin ƴan kasuwa da ake zargin abinci ne.za a fitar da shi ƙasashen waje.
Asali: Legit.ng