Tsohon Minista da Ake Bincike Ya Kai Karar EFCC, Yana Neman Diyyar N1bn a Kotu

Tsohon Minista da Ake Bincike Ya Kai Karar EFCC, Yana Neman Diyyar N1bn a Kotu

  • Olu Agunloye ya koma yana karar EFCC a kotu saboda sun yi shelar yana cikin mutanen da ake nema da zargin rashin gaskiya
  • Tsohon ministan tarayyar ya ce abin da hukumar yaki da rashin gaskiya tayi ya jawo masa abin kunya da batanci ba kan doka ba
  • Adeola Adedipe SAN shi ne ya tsayawa Agunloye a kotun tarayya, yana neman kotu ta tilastawa hukumar EFCC biyan diyyar N1bn

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Olu Agunloye wanda ya yi Ministan makamashi da karafuna a gwamnatin Najeriya ya shigar da karar hukumar EFCC a kotu.

The Nation ta ce Dr. Olu Agunloye zai yi shari’a da EFCC ne saboda hukumar ta wallafa sunansa cikin jerin mutanen da ake nema.

Olu Agunloye
Olu Agunloye ya kai EFCC kara a Kotu a Abuja Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jami'an EFCC v Olu Agunloye

Tsohon Ministan ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/167/2024 a babban kotun tarayya da ke Abuja ta hannun wasu lauyoyi.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adeola Adedipe, SAN ita ce shugabar lauyoyin da suka tsayawa tsohon ministan kasar da ake bincike a kan kwangilar Mambila.

Kamar yadda jaridar ta kawo rahoto, Agunloye ya hada da Ministan shari’ kuma babban lauyan gwamnati a wadanda yake tuhuma.

Yaushe za a fara shari'a da EFCC?

Alkalin da zai saurari karar shi ne Mai shari’a Emeka Nwite, kuma an tsaida 18 ga watan Afrilu a matsayin lokacin da za a fara zama.

Tsohon ministan ya ce EFCC ba ta da ikon cusa sunan shi a shafinta na yanar gizo a jeringiyar wadanda ake nema ruwa a jallo a kasar.

Agunloye yana ganin sassa na 34({1)(a), 35, 37, 39, 41 da na 42 na kundin tsarin mulki da dokar shari’a ba su jami'an EFCC hurumin nan ba.

EFCC ta cire sunan Olu Agunloye

Kara karanta wannan

Ba za mu yarda ba: Rayuwar Murja Kunya tana fuskantar Barazana Inji Lauyoyi

Saboda haka The Cable ta ce lauyoyin toshon Ministan da ake rikici da shi sun nemi hukuma ta cire sunan shi a wadanda ake cigiya.

Adeola Adedipe SAN tana so Alkali ya bada umarnin goge sunan wanda suke karewa daga shafin EFCC da jaridu da wasu wurare.

‘Dan siyasar yana so a biya shi diyyar N1bn saboda a cewarsa rikicin Messrs Sunrise Power da gwamnatin kasar ya bata masa suna.

Za a rufe asusun mutane a banki

Idan ana zancen kudi, an ji labari babu mamaki a toshe asusu tsakanin miliyan 70 zuwa 85 a bankunan kasuwa saboda umarnin CBN.

Duk asusun da bai da NIN ko BVN yana cikin barazana, za a hana shiga da ficen kudi a cikinsa kamar yadda babban banki ya sanar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng