Mayakan ISWAP Sun Farmaki Manoma a Borno, Sun Halaka Mutum 3 Da Sace Kekuna 50
- Akalla rayukan mutane uku ne suka salwanta bayan wasu tagwayen bam sun fashe a karamar hukumar Damboa, jihar Borno
- Bama-baman sun tashi ne a lokacin da dakarun tsaro ke aikin kakkabe mabuyar mayakan kungiyar ta'addancin sakamakon taka su da aka yi bisa kuskure
- Haka kuma, mayakan ISWAP sun farmaki manoma tare da sace masu kekuna 50 bayan sun halaka mutum biyu a cikinsu
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Borno - Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane uku ne suka rasa ransu a wasu tagwayen hare-hare da mayakan kungiyar ta'addanci, wato ISWAP suka kai a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.
An tattaro cewa wasu 'yan banga biyu sun rasa ransu samakon tashin abin fashewa a wani samame da dakarun soji suka kai yankin Kudancin Damboa a ranar Alhamis.
Wata majiya ta bayyana cewa wasu 'yan farar hula da ke tuka babura sun yi tuntube da ababen fashewa, wanda nan take ya halaka mutum biyu, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewar an kwaso gawarwakin mamatan zuwa garin Damboa a safiyar jiya Juma'a, domin jana'izarsu daidai da koyarwar Musulunci.
Ya ce:
"Mun rasa 'yan farar hula biyu da ke taimaka mana a yayin kai samame sakamakon tashin abun fashewa da mayakan ISWAP suka binne a yankin Damboa."
Yadda mayakan ISWAP suka addabi manoma a Borno
Haka kuma, an tattaro cewa mayakan ISWAP suna ta addabar manoma tun a ranar Litinin.
An tattaro cewa kungiyar ta'addanci ta kwace kekunan fiye da 50 daga hannun manoma cikin kwanaki biyar da suka gabata.
"A makon nan kadai, manoma sun rasa babura kimanin guda 57 a hannun mayakan ISWAP da ke kai masu hari a kullun kan gonakinsu. Sun yi barazanar kashe su idan har basu sallama masu kekunan ba.
"Sun karbe gaba daya kudadensu, wayoyi da ruwa," cewar daya daga cikin wadanda lamarin ya ritsa da su.
Me rundunar sojoji tace kan harin?
Zuwa yanzu, rundunar soji bata saki kowani jawabi kan harin na baya-bayan nan ba, Trust Radio ya ruwaito.
Bam ya halaka mutane a Borno
A wani labari makamancin wannan, mun ji cewa wasu leburori biyu sun rasa ransu bayan bam guda biyu sun tarwatse a wurin aiki da ke karamar Dikwa a jihar Borno.
Rahotanni sun tabbatar da cewa bam na farko ya fashe ne a makarantar firamare ta Koibe da ke jihar, cewar TheCable.
Bam din ya fashe lokacin da wani labura ya dauko bulolluka zuwa wani bangare na makarantar ashe bai san ya na dauke da bam din ba.
Asali: Legit.ng