Gwamnatin Tinubu Ta Dura Kan ’Yan Crypto, Ta Kakaba Wa Binance Tarar Dala Biliyan 10

Gwamnatin Tinubu Ta Dura Kan ’Yan Crypto, Ta Kakaba Wa Binance Tarar Dala Biliyan 10

  • Gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta ci kamfanin Binance tarar dala biliyan 10 a wani yunkuri na ganin ta karya farashin dala
  • Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasar shawara ta fuskar yada labarai ya ce an ci Binance tarar ne saboda karya dokokin cinikayya na kasar
  • Onanuga ya ce kamfanin ya yi amfani da wasu ƴan ƙasar wajen kayyade farashin canjin Naira wanda hakan ya jawo kasar ta tafka asara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta bukaci tarar dala biliyan 10 daga Binance, wani shahararren dandalin hada-hadar kudaden 'cryptocurrency.'

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara kan yada labarai da tsare-tsare ya tabbatar da hakan a safiyar Juma’a a wata hira da BBC.

Kara karanta wannan

Yadda aka damke shugabannin kamfanin Binance daga kasar waje a yunkurin karya Dala

Gwamnatin Najeriya ta ci kamfanin Binance tarar dala biliyan 10
Bayo Onanuga ya ce Binance ta jawo Najeriya ta tafka asara mai yawa. Hoto: Getty Images, @officialABAT/X
Asali: Getty Images

Mai taimaka wa shugaban kasar ya ce an bukaci tarar ne bayan kama kamfanin Binance da aika laifukan da taimaka wajen faduwar darajar Naira a 'yan kwanakin nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Onanuga, Binance ya samu riba mai yawa daga “mu’amalar cinikayya da 'yan kasar wanda ba ta dace ba” yayin da Najeriya ta tafka asara mai yawa.

Tawagar Binance na ba gwamnati hadin kai

Premium Times ta ruwaito Onanuga na ikirarin cewa kamfanin Binance ba shi da rajista a Najeriya kuma ba shi da wani ofishi a kasar.

Ya yi zargin cewa mutane sun yi amfani da dandalin wajen kawo rashin daidaiton farashin dala da Naira; abun da ya ce ya yi illa ga darajar kudin kasar.

Ya kuma yi bayanin cewa tawagar Binance a halin yanzu na ba gwamnatin Najeriya hadin kai ta hanyar samar da bayanai masu amfani, kuma tuni ta dakatar da hada-hadar naira a dandalin.

Kara karanta wannan

Babban labari: Gwamnatin Najeriya ta cafke jami'an manhajar Binance, an samu ƙarin bayani

An zargi Binance da kayyade farashin kudi

Yayin da yake nuni da cewa gwamnati na ganin mummunan tasirin ayyukan Binance a Najeriya, Onanuga ya ce:

“Binance yana kayyade farashin canjin kudin Najeriya a dandalin, wanda ya sabawa doka. Babban bankin Najeriya ne kadai ke da ikon kayyade farashin canji ga Najeriya.
Binance yana goyon bayan mutane da yawa da ke tsawwala farashin canji wanda ya yi tasiri sosai a ƙasar a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin daidaita tattalin arziki.

Gwamnatin Najeriya ta cafke shugabannin Binance

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta ba da umarnin kama wasu shugabannin kamfanin Binance da suka shigo ƙasar don tattaunawa da gwamnatin.

Bayan rashin jituwar da aka samu da jami'an a wani zama da aka yi da su a Abuja, an ruwaito cewa jami'an tsaro sun kwace fasfo din su.

Gwamnatin Najeriya ta bukaci shugabannin kamfanin da su bayar da bayanan asusun duk wani ɗan Najeriya da ke hada-hadar kudi a dandalin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.