Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala

Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala

- Aikat alaifin fitsara ya sanya 'yan Hisbah yiwa wasu mata kamun kazar kuku

- Hukumar ta kuma kame katan 300 na barasa

A yau Litinin ne humumar Hisbah ta bayyana cafke wasu yan mata a cikin birnin kano bisa lafin rashin ɗa'a.

Kamfanin dillacin labarai ta kasa (NAN) ya bayyana cewa dukkanin wani laifi na rashin ɗa'a ya saɓawa dokar shari'a a jihar Kano, wanda shi ne maƙasudin da yasa hukumar ta yi awon-gaba dasu.

Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala
Hukumar Hisbah ta cafke wasu 'yan mata 5 bisa laifin baɗala

Kakakin hukumar ta hisbah Malam Adamu Yahaya ya bayyanawa NAN cewa hukumar ta cafke 'yan matan ne a wani sumamane na musamman da suka kai a unguwar Ɗanbare dake karamar hukumar Gwale da misalin karfe 9 na dare.

KU KARANTA: Ta hada baki da mahaifiyarta sun kashe mahaifinta

Ya ce mutanen unguwar ne suka kawo korafin cewar akwai wasu 'yan mata guda biyar da ake zargin sun kama hayar gida tare da samarinsu, wanda suke baɗala iri-iri a gidan.

Ya kara da cewa yan matan da aka cafke shekarunsu bai wuce 18 zuwa 20 ba. "Mutanenmu sun je unguwar ne da misalin karfe 9 na dare sannan suka shiga har cikin gidan suka kama yan matan" kamar yadda Yahaya ya bayyana.

Mai magana da yawun hukumar, ya bayyana cewa zasu kira iyayen yaran domin su zo a ja musu kunne akan idonsu tare da yin yarjejeniyar cewa ba zasu ƙara aikata laifin da ake tuhumarsu ba, saboda wannan shi ne karo na farko da suka shiga hannun hukumar.

Yahaya ya ƙara da cewa sun samu bayanai da dama cewa akwai yan matan da aka kawo su domin yin fasiƙanci wai da sunan murnar sallah tun daga Abuja, kuma ya bayyana cewa hukumar ta yi nasarar kwace wasu kwalaben Giya har kimamin katan 300 a unguwar Na'ibawa, dake karamar hukumar Tarauni.

Ya ce hukumar zata bayyana lokacin da zata ƙona wannan kayan laifi da ta kama sannan kuma su masu laifin za a tusa ƙeyarsu zuwa gaban alkali.

Daga karshe ya ja hankalin matasa a garin na Kano da su zamo masu ɗa'a da tsoron ubangiji domin su samu ingantacciyar rayuwa a nan gaba. ƙara kira tare da jan hankalin iyaye da su sake sa ido wajen tarbiyyar 'ya'yansu, domin su kasance abin misali a gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel