Babbar Nasara: Asirin Wasu Ƴan Bindiga 15 Ya Tonu, Sun Fara Sakin Bayanai a Jihar Arewa
- Ƴan sanda sun damƙe mutum 15 da ake zargin ƴan bindiga ne da masu hannu a aikata miyagun laifuka jihar Neja
- Kwamishinan ƴan sanda na jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ya ce jami'an tsaron sun kuma kwato muggan makamai da alburusai
- Ya ce ɗaya daga cikin cikin waɗanda suka shiga hannu ya ba da haɗin kai yayin bincike, ya faɗi sunayen ƴan tawagarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Rundunar ‘yan sandan jihar Neja ta kama wasu mutane 15 da ake zargin ƴan bindiga ne da kuma masu aikata miyagun ayyuka a jihar.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, Shawulu Ebenezer Danmamman, ne ya bayyana haka jiya Alhamis, 29 ga watan Fabrairu, 2029, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Majalisar dattawa ta bada umarnin a ɗauki mutum 10 aikin ƴan sanda a kowace ƙaramar hukuma, ta faɗi dalili
Ya kuma kara da cewa jami'an ƴan sandan sun kwato manyan bindigu da alburusai daga hannun waɗanda ake zargin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce sun samu wannan nasara ne bayan tattara bayanan sirri, inda jami'an ƴan sanda suka kai samame maɓoyar ƴan bindigan kuma suka damƙo su.
Yadda jami'an tsaro suka kama ƴan bindiga
Kwamishinan ya ce dakarun sashin dabaru da haɗin guiwar ƴan banga ne suka farmaki sansanin da ke ƙauyen Tuna a kan titin Gawu-Babangida a ƙaramar hukumar Gurara.
Ƙarƙashin shugaban ofishin ƴan sanda na Giwa, jami'an tsaron sun kama wani mai suna, Abdulrahman Abubakar ɗauke da bindogar Ak-47 yayin da sauran suka arce.
CP ya ce yayin bincike, ya ambaci sunayen ƴan tawagarsa da suka haɗa da Hari, Isyaku, da Suleiman, dukkansu ‘yan kauyen Tuna.
Haka nan ya faɗa wa ƴan sanda cewa bindigar da aka kama shi da ita ta dan uwansa ne mai suna Rabo da ke kauyen.
Masu garkuwa sun yi wa ɗan ƙasuwa barazana
Bayan haka, CP ya ce sun samu rahoton wasu mutum 4 da ake zargin masu garkuwa ne sun yi wa wani dan kasuwan kauyen Bako-Mission, gundumar Pissa ta karamar hukumar Borgu barazana.
A kalamansa ya ce:
"Jim kaɗan bayan samun wannan rahoto, yan sanda tare da haɗin guiwar yan banga suka dira wurin, suka yi artabu da ƴan bindigan kuma suka ceto wata mata.
"Daga nan tawagar jami'an tsaro sun kewaye jejin, inda suka kashe ɗan bindiga ɗaya kuma suka kwato bindigar Ak-47."
Nasarorin da sojoji suka samu a wata ɗaya
A wani rahoton na daban Sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka ƴan ta'adda sama da 900, sun kana wasu 621 a sassa daban-daban na kasar nan a watan Fabrairu.
Hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ce ta bayyana haka yayin da take zayyana nasarorin rundunar soji a tsawon wata ɗaya ranar Alhamis.
Asali: Legit.ng