Ana Samun Kusan N200m a Awa 1 Kowace Rana a Tashar Apapa Inji Hukumar Kwastam
- Ba kananan kudi hukumar kwastam ta ke samu a Najeriya ba duk ana korafin cewa an rufe wasu daga cikin iyakokin kasar
- A tashar kwastam da ke Apapa a jihar Legas kadai, ana samun kimanin N200m a sa’a guda, za a iya tashi da N140bn a duk wata
- Bayan kudin shiga da gwamnatin tarayya ta ke samu ta hukumar kwastam, jami’ai suna tare kayan da za a shiga ko fita da su
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A lokacin da ake kukan babu kudi a Najeriya, hukumar kwastam tana cigaba da namijin kokari sosai a wannan bangare.
Hukumar kwastam mai kula da iyakokin kasar nan ta sanar da abubuwan da mafi yawan mutane ba su sani ba a shafinta na X.
38% na kudin kwastam suna Apapa
Bayanan da aka samu a dandalin ya nuna irin makudan biliyoyin da suke shiga asusun tarayya ta iyakokin da ke jihar Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar kwastam kimanin N200m ake samu a kowace rana daga tasharta da ke Apapa, ita ke samar da 38% na kudin shiga.
Lissafin ya nuna a cikin awanni 24 da ake da su a kullu-yaumin, hukumar za ta iya tatso kusan Naira biliyan zuwa baitul-mali.
Bayanin hukumar kwastam a X
“Kun san cewa Hukumar kwastam, ta reshen Apapa kurum tana tatsar N198,802,021 a kowane awa da kuma N4,771,248,513 a kowace rana?”
Gwamnati tana samun kudin shiga
Ba a nan bayanan suka tsaya ba, a shafin na X da aka fi sani da Twitter ne aka fahimci darajar tashar Oyo/Osun a gidan kwastam.
Jami’an Oyo/Osun ne a kan gaba idan maganar samun kudin shiga yayin da ake zargin wasu ma'aikata a cikin badakalar N12bn.
Hobbasan kwastam a bakin iyakoki
Wani abin da aka jahilta shi ne yadda ake kokari wajen karbe haramtattun kayan da aka saba shigowa da su daga kasashen ketare.
Shugaban jami’an Adamawa/Taraba, Salisu Abdullahi ya shaida cewa sun karbe kayan da darajarsu ta kai N13.352m kwanan nan.
Man fetur da shinkafar kasar waje suna cikin kayayyakin da kwastam suka tare a iyakoki bayan sun kara tsada a kasuwanni.
Babban jami’in yake cewa a makonni biyun da suka wuce, sun cafke mutanen da ke kokarin shiga man fetur zuwa kasar Kamaru.
Rikicin gwamnatin Najeriya da Binance
Ana da labari cewa sabanin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kamfanin nan na Binance yana neman ya karu a maimakon a daidaita.
Tun jiya aka tsare wani ‘Dan Amurka da Bature da suka zo a tattauna kan takunkumin da aka kakabawa Binance a kan tashin Dala.
Asali: Legit.ng