Oronsaye: Abin da Zai Faru da Ma'aikatan Gwamnati Wajen Rushe Hukumomi Inji Minista
- Gwamnatin tarayya ta yi karin haske a game da shirin da ake yi na rusa ko narkar da wasu ma’aikatu da hukumomin da ke kasar
- Ministan labarai da wayar da kai ya ce ma’aikatun da abin zai shafa ba su da amfani ne ko kuwa an samu maimai a aikin na su
- Alhaji Mohammed Idris ya shaidawa ma’aikata cewa gwamnati ba tayi hakan domin korar ma’aikata ba, sai dai domin yin gyara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Ministan labarai da wayar da kan al’umma, Mohammed Idris, ya yi magana a game da aiwatar da aikin kwamitin Steven Oronsaye.
A ranar Laraba, The Nation ta rahoto Mohammed Idris yana cewa mutane ba za su rasa aikinsu saboda an taba ma’aikatun gwamnati ba.
Ministan ya sanar da haka ne a wani jawabi na musamman da ya fitar ta bakin mai taimaka masa wajen yada labarai, Rabiu Ibrahim.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin yin garambawul a ma'aikatun gwamnati
Gwamnati ta ce za a taba hukumomi da ma’aikatun ne saboda a gyara tsarin aikin gwamnati kuma a rage batar da makudan kudi.
A jawabin da ya yi wa manema labarai, ya ce wasu ma’aikatan da za a taba ba su da wani amfani a yau ko dai an samu mai-man aiki.
Oronsaye: Bayanin Ministan labarai a Abuja
"Kwanaki biyu da suka wuce shugaban kasa ya amince da hanyar da za a bi wajen rage kashe kudin tafiyar da gwamnati ta hanyar aiwatar da rahoton Oronsaye – shekaru 12 bayan an gabatarwa shugaban kasa a lokacin, Dr. Goodluck Jonathan."
"Wannan karara ya nuna jajircewar shugaban kasa wajen kula da harkar kudi da tafiyar da gwamnati yadda ta dace ta hanyar sake duban ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati."
- Mohammed Idris
Idris yake cewa sai da gwamnatin tarayya tayi bincike kafin daukar matakin nan. A baya an zarge ta da garajen wajen kawo tsare-tsare.
Ba za a raba mutane da hanyar neman abincinsu ba, za a duba bukatun ‘yan kasa, amma ministan ya ce kishin Najeriya za a sa a gaba.
Oronsaye ba zai sa a rasa aiki ba
An rahoto Sanata Shehu Sani yana cewa amfani da shawarar Steven Oronsaye zai jawo mutane su rasa aiki a gwamnati a kasar.
Tsohon 'dan majalisar ya yarda wannan zai yi maganin facaka da kudi a gwamnati, amma yana tsoron za a talauta wasu masu aiki.
Asali: Legit.ng