An Gurfanar da Sojojin Najeriya a Gaban Kotu Kan Zargin Sayar da Makamai da Wasu Munanan Laifuka

An Gurfanar da Sojojin Najeriya a Gaban Kotu Kan Zargin Sayar da Makamai da Wasu Munanan Laifuka

  • Rundunar sojin Najeriya ta gurfanar da sojoji 16 da jami’i guda ɗaya a gaban kotu bisa samunsu da laifin aikata rashin ɗa’a
  • An tattaro cewa ana yi wa waɗannan jami’an shari’a ne bisa laifukan fashi da makami, sayar da makamai da sauransu
  • Kotun ta fara sauraron ƙarar ne a ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu a sansanin rundunar sojoji ta 3 da ke Maxwell Khobe a ƙaramar hukumar Bassa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Bassa, jijar Plateau - An fara zaman shari’ar wasu sojoji 16 da jami’i guda ɗaya a jihar Plateau.

Ana tuhumar su da laifuffuka da suka haɗa da fashi da makami, kisan kai, mallaka ba bisa ƙa’ida ba da kuma sayar da makamai da alburusai, waɗanda suka saba wa aikinsu na runduna ta 3, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: An yi hasashen Dala za ta kai N4000 kafin karshen 2024, an fadi dlalili

An gurfanar da sojoji a gaban kotu
Ana zargin sojojin dai da sayar da makamai da aikata fashi da makami Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

A ranar Talata, 27 ga watan Fabrairu ne kotun sojin ta fara aiki a sansanin rundunar sojoji ta 3 na Maxwell Khobe a ƙaramar hukumar Bassa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manjo Aminu Mansur Mairuwa, muƙaddashin darakta mai kula da harkokin shari’a na rundunar sojan Najeriya ta 3, ya jaddada ƙudirin rundunar na tabbatar da ɗa’a a yayin ƙaddamar da babbar kotun sojin.

Meyasa aka fara zaman kotun?

Ya bayyana cewa, mutanen da ake zargi an bi su da hanyoyin da suka dace, wanda ke nuna mutunta doka da bin ƙa’idojin adalci da ake da su.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Mairuwa ya ce:

"Muhimmancin shine tabbatar da cewa jami'an soji a koyaushe suna aiki a cikin iyakokin ayyukanmu, ƙa'idojin mu, da mutunta kyawawan ayyuka na ƙasa da ƙasa."

Shugaban kotun sojin, Birgediya Janar Liafis Bello, ya jaddada muhimmancin ɗa'a da nuna ƙwarewa a cikin rundunar sojojin Najeriya.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Wata mata ta shiga gagarumar matsala bayan ta ci zarafin jami'ar 'yar sanda a Legas

Ya bayyana cewa kafa kotun sojin tsari ne na yau da kullun don kiyaye ƙa'idojin hukumar.

Za a fara shari’ar ne a ranar 6 ga watan Maris, 2024, bayan da kotun ta ɗage ci gaba da sauraron ƙarar.

An Cafke Sojojin Bogi a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar ƴan sandan jihar Legas ta cafke wasu sojojin bogi guda biyu wadanda ake zargi da yin barazanar kashe wani mutum da wuƙa.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya ce waɗanda ake zargin suna hannun ƴan sanda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng