Tsadar Rayuwa: Kabilar Igbo Sun Fadi Babban Dalilin Kin Shiga Zanga-Zanga, Sun Goyi Bayan Tinubu
- Kabilar Igbo sun bayyana dalilin da ya sa ba za su shiga zanga-zangar da ake yi a fadin Najeriya ba baki daya kan tsadar rayuwa
- Wata kungiya a yankin Kudu maso Kudancin Najeriya ta bayyana dalilinta inda ta ce rashin adalcin da aka musu ya fi karfin zanga-zangar
- Ta ce duk da halin kunci da suke ciki a yankin, ‘yan kabilar sun ki shiga zanga-zangar inda hakan ya jawo kace-nace
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Enugu - Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a fadin Najeriya, wata kungiya a yankin Kudu maso gabashin Najeriya ta fadi dalilin kin shiga zanga-zangar.
Kungiyar mai suna South East Development Peace Initiative (SPDI) ta shawarci kabilar Igbo a Najeriya da su gujewa zanga-zangar.
Menene dalilinsu na kin shiga zanga-zangar?
Ta ce duk da halin kunci da suke ciki a yankin, ‘yan kabilar sun ki shiga zanga-zangar inda hakan ya jawo kace-nace, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kungiyar, Hon. Vitus Okechi ya ce rashin adalcin da ake yi wa yankin da kabilar a Najeriya ya fi karfin su yi zanga-zanga.
Vitus ya ce duk da wahalar da ake sha amma rashin adalci da ake yi wa kabilar Igbo bai kamata su fito don nuna wata damuwa ba.
Okechi wanda shugaban karamar hukuma ce a jihar Enugu ya ce babu dalilin yi wa gwamnatin Tinubu bore don ana cikin wani hali.
Sun nuna goyon bayansu ga Tinubu
Ya ce ya yi mamaki yadda ‘yan Najeriya ke zanga-zanga duk da halin da ‘yan yankin ke ciki na nuna wariya da cin zarafi wanda ya fi yunwa matsala.
Okechi ya ce Igbo sun fi kowa shan wahala inda ko wane matsala da su ta ke rutsawa inda ya ce ko a jihohi an nuna musu wariya.
Har ila yau, ya ce za su ci gaba da goyon bayan Shugaba Tinubu inda ya ce sun san shugaban ya san meye ya ke yi kuma zai kawo sauyi.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin wani hali wanda ya jefa ‘yan kasar a cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa cewar Vanguard.
An gano ‘yan sanda na raba ruwa da biskit
Kun ji cewa yayin da ake zanga-zanga a birnin Legas, an gano ‘yan sanda na raba ruwa da biskit ga masu zanga-zangar.
Wannan lamari ya bai wa mutane mamaki inda suka ce bai dace mutane su karbi wannan kyautar ba tun da zanga-zanga ake yi.
Asali: Legit.ng