Tsadar Rayuwa: Bidiyon ‘Yan Sanda Su Na Raba Wa Masu Zanga-zanga Biskit da Ruwa a Legas
- Jama'a sun yi martani yayin da ake tsaka da zanga-zanga inda rundunar 'yan sanda ke raba wa mutane ruwa
- An gano rundunar ta na raba ruwa da kuma biskit yayin zanga-zanga a birnin Legas a yau Talata 27 ga watan Faburairu
- Wannan na zuwa ne yayin da kasar ta rikice a yau Talata 27 ga watan Faburairu kan tsadar rayuwa a kasar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas - Yayin da ake ci gaba da zanga-zanga a Legas, an gano 'yan sanda na raba biskit da ruwa ga mutane.
Masu zanga-zangar sun cika titunan birnin Legas ne don nuna rashin jin dadin halin kunci da 'yan kasar ke ciki.
Menene dalilin zanga-zangar a Najeriya?
A zanga-zangar wanda kungiyar NLC ke jagoranta ta kuma yi korafi kan rashin cika alkawarin da suka yi da gwamnatin bayan cire tallafin mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
TheCable ta tattaro cewa an gano lokacin da rundunar ke raba ruwan da biskit mutanen ke ihu su na cewa sai 'yan sandan Najeriya.
Wasu mutane sun caccaki tsarin inda suke cewa ta yaya gwamnatin za ta dauki mutane da gaske bayan halin da suka nuna.
Suka ce hakan zai kara saka masu mudafun iko gane cewa ba da gaske ake ba yunwa ce kawai ke damun jama'a.
Yadda ake gudanar da zanga-zangar a Najeriya
Wannan na zuwa ne yayin da kasar ta rikice a yau Talata 27 ga watan Faburairu kan tsadar rayuwa.
An ruwaito cewa zanga-zangar ta samu karɓuwa sosai musamman a jihohin Kudancin Najeriya.
Har ila yau, a jihohin Kano da Kaduna da Gombe da Plateau da ke Arewacin kasar jama'a sun fito don nuna goyon baya.
Tinubu zai jiki matasa da kudade
A baya, kun ji cewa Gwamnatin Tarayya ta shirya biyan matasa da ba su da aikin yi da alawus duk wata a Najeriya.
Shirin zai taimakawa matasan ne da ke da kwalin digiri ko na kwalejin ilimi don tsame su daga kunci.
Wannan na zuwa ne yayin da ake cikin mummunan yanayi a Najeriya kan tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng