Kungiyar Kwadago Ta Fara Gudanar da Zanga-Zangar Gama Gari Kan Tsadar Rayuwa
- Kungiyar kwadago ta fara zanga-zangar gama gari saboda tsadar rayuwa da ake fama da shi a Najeriya
- Mambobin kungiyar sun mamaye unguwanni a jihar Legas, a yau Talata, 27 ga watan Fabrairu, domin nuna bacin ransu kan halin da ake ciki na matsin tattalin arziki
- An dai yi zama tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya a ranar Litinin, amma aka tashi baran-baran ba tare da an cimma matsala daya ba
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Lagos - Kungiyar kwadago ta kasa ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar TUC ta ce ba za ta shiga wannan zanga-zangar ta 'yan kwadago ba.
Mambobin kungiyar NLC sun mamaye unguwanni a jihar Legas domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwar da ake fama da shi a kasar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan kwadagon na kuma zanga-zanga akan gazawar gwamnati, wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a ranar 2, ga watan Oktoban 2023, bayan cire tallafin man fetur.
Me yasa kungiyar kwadago ke zanga-zanga a Najeriya?
Wannan mataki ya biyo bayan cikar wa'adin kwanaki 14 da suka bai wa gwamnatin tarayya domin ta dauki matakai kan mawuyacin halin da al'ummar kasar ke ciki.
An tashi baran-baran a taron da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago a daren jiya Litinin, inda kungiyar ta sha alwashin fara zanga-zangar da ta yi niya.
Mambobin kungiyar ta NLC da yawansu sun mamaye karkashin gadar Ikeja, inda aka gano su suna wake-wake da raye-raye yayin da suke kira ga gwamnati da ta saurari bukatunsu.
Ana sanya ran zanga-zangar za ta ci gaba a gobe Laraba, 28 ga watan Fabrairu, jaridar Punch ta ruwaito.
NLC ta mika bukatarta wajen gwamnati
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya ba ta iya shawo kan kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC ta fasa shirya zanga-zangarta ba.
Duk da an zauna da manyan jami’an gwamnati, The Cable ta ce shugabannin ma’aikatan sun cije sai sun cigaba da zanga-zanga.
Asali: Legit.ng