Akpabio: Gaskiya Tayi Halinta Kan Zancen Rabawa Gwamnoni N30bn Saboda Rage Yunwa

Akpabio: Gaskiya Tayi Halinta Kan Zancen Rabawa Gwamnoni N30bn Saboda Rage Yunwa

  • Godswill Akpabio ya janye kalaman da ya yi kwanakin baya, yana ikirarin jihohi 36 sun samu biliyoyi daga asusun tarayya
  • Shugaban majalisar dattawan ya ce an raba kudin ne domin a magance matsalar yunwa, ashe zancensa ba gaskiya ba ne
  • Sanata Godswill Akpabio ya bada hakuri ta bakin mai magana da yawunsa bayan zama da ya yi da shugaban gwamnoni

Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ba gwamnonin jihohi hakuri a game da kalaman da ya yi kwanaki.

A makonnin da suka wuce aka rahoto Godswill Akpabio yana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta rabawa jihohi karin N30bn.

N30bn:Shugaban majalisa
N30bn: Godswill Akpabio zaune a kujerar shugaban majalisa Hoto: The Senate President - Nigeria
Asali: Facebook

N30bn: Godswill Akpabio ya yi kuskure

A yau Punch ta kawo labari cewa Sanata Godswill Akpabio ya lashe aman da ya yi, ya kuma nemi afuwar gwamonin Najeriyan.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya tona boyayyun bayanai a kan bashin da Buhari ya karbo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar ya fitar da jawabi ta bakin Eseme Eyiboh, ya nemi afuwa inda ya kara da cewa yana ganin girman gwamnonin.

Hadimin Akpabio ya fitar da jawabi

Eseme Eyiboh ya ce mai gidansa ya yi nadamar abin da ya fada a lokacin da ake karbar rahoton aikin wasu kwamitocin majalisa.

Godswill Akpabio ya yi magana game da rade-radin cewa gwamoni sun samu N30bn domin magance matsalar yunwa a jihohinsu.

Eyiboh ya ce Akpabio bai nufin komai illa ganin gwamnoni sun hada kai da gwamnatin Bola Tinubu wajen gyara tattalin arziki.

Akpabio ya yabawa Gwamnonin da ya ce an ba N30bn

Shugaban majalisar dattawan ya ce ya sani kuma ya yaba da irin kokarin da gwamnoni suke yi wajen rage radadin rayuwa.

Jawabin hadimin shugaban majalisar tarayyan yake cewa an san rawar da gwamnoni suke takawa wajen taimakawa Tinubu.

Kara karanta wannan

Matakin Tinubu 1 ya jefa Najeriya cikin wahala Inji Sakataren Gwamnatin Buhari

Kalaman sun fito ne bayan Akpabio ya zauna da shugaban kungiyar gwamnoni na kasa, Mai girma AbdulRahman AbdulRazaq jiya.

Akpabio ya yi kira ga gwamnonin cewa ka da wannan sabani ya janye masu hankali.

Gwamnoni sun karyata zancen Akpabio

Tun kwanaki kun ji labari cewa jami’an gwamnatoci sun tabbatar da cewa zancen ba jihohi karin Naira Tiriliyan 1.08 bai da wani tushe.

Babu wani Gwamna da ya fito ya ce da gaske ne an rabawa kowace jiha karin wasu N30bn, sai dai aka ji suna ta karyata wannan batu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng