Babu Wanda Zai Hana: NLC Ta Nemi Bukata 1 Daga Gwamnati Wajen Shirya Zanga Zanga

Babu Wanda Zai Hana: NLC Ta Nemi Bukata 1 Daga Gwamnati Wajen Shirya Zanga Zanga

  • Shugabannin NLC ba su yarda su fasa yi zanga-zangar lumuna ba duk da taron da aka yi domin gwamnatin tarayya ta lallashe su
  • Sakataren gwamnatin tarayya, Ministoci da DG DSS sun zauna da wakilan NLC da TUC da sauran kungiyoyin ‘yan kasuwa da ma’aikata
  • An tashi taron ba tare da an yi wata nasara ba, shugaban kungiyar NLC ya bukaci gwamnati ta ba su kariya wajen zanga-zangarsu

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Gwamnatin tarayya ba ta iya shawo kan kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC ta fasa shirya zanga-zangarta ba.

Duk da an zauna da manyan jami’an gwamnati, The Cable ta ce shugabannin ma’aikatan sun cije sai sun cigaba da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

NLC ta yi bazaranar ɗaukar mataki 1 idan aka farmaki masu zanga-zangar lumana a ƙasar

Zanga-zanga
NLC za ta cigaba da zanga-zanga Hoto: Getty Images/Buhari Sallau
Asali: UGC

Zanga-zanga: SGF ya hadu da 'yan kwadago

Sakataren gwamnatin tarayya watau George Akume ya jagoranci wakilan gwamnati domin a zauna da manyan ‘yan kwadago.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin NLC da TUC ta ‘yan kasuwa da sauran ma’aikatan Najeriya sun halarci zaman duk da TUC ba ta cikin zanga-zangar.

Matsayar NLC a kan zangar-zangar lumuna

A karshen taron da aka yi, Joe Ajaero wanda shi ne shugaban NLC, ya shaida cewa ba za su fasa yin zanga-zangar lumunar nan ba.

An rahoto Joe Ajaero yana cewa za su yi zanga-zangar gama-garin ne domin nuna rashin jin dadinsu a kan matsin tattalin arziki.

Ana bukatar tsaro wajen zanga-zanga

Jagoran ya shaidawa ‘yan jarida hakki ya rataya a wuyan kowane bangare wajen ganin an yi zanga-zangar ba tare da rikici ba.

Shugaban kungiyar NLC ya bukaci gwamnatin tarayya ta ba su jami’an tsaro kamar yadda tsari da dokar kasa suka bada dama.

Kara karanta wannan

‘Yan kwadago sun yanke matsaya kan hakura da zanga-zanga saboda barazanar DSS

"Za a yi zanga-zangar kuma nauyi ne a tsarin mulki a wuyansu (gwamnati) domin tabbatar da cewa an yi zanga-zangar lafiya"
"Muna da bukatun da dole mu gabatar, saboda haka watakila gobe (Talata) idan mun gabatar da bukatun, ‘yan jarida za su samu takardar.”

- Joe Ajaero

Daily Trust ta ce an yi zaman ne da Ministocin noma, kasafi, kwadago, shari’a, shugabar ma’aikata da kuma Darekta Janar na DSS.

ASUU za ta shiga zanga-zangar NLC

Legit ta ji labari kungiyar malaman jami’a watau ASUU ta reshen ABU Zariya ta fitar da sanarwa cewa za ta shiga zanga-zangar nan.

Kwanaki da biyan malaman jami’ar, sai ga 'yan ASUU suna goyon bayan kungiyar NLC wajen kokawa da tsadar rayuwar da aka shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng