Oronsaye: Wasu Ma’aikatu da Hukumomi 45 da Gwamnatin Tarayya Za Ta Iya Rusawa
- Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni a dabbaka shawarwarin da kwamitin Steve Oronsaye ya ba gwamnatin Goodluck Jonathan
- Sabon shugaban Najeriyan ya dauki wannan mataki ne a wajen zaman majalisar FEC da aka yi domin rage kashe kudi a kasar
- An nemi hada NEMA da sauran hukumomin da ke kula da ‘yan gudun hijira a Najeriya, akwai hukumomi 30 da za a iya soke su
Abuja - Tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ya kawo shawarar a soke wasu ma’ikatu, ya kuma nemi a dunkule wasunsu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince a aiwatar da shawarar Steve Oronsaye a gwamnatin tarayya bayan an yi watsi da aikin.
Gwamnatin Tinubu za ta rage kashe kudi
Matakin ya zo ne jim kadan bayan Atiku Abubakar ya bada irin wannan shawara, ya ce Bola Tinubu ya yi koyi da shugaban Argentina.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit ta dubi shawarwarin da kwamitin Steve Oronsaye ya gabatar mai shafi 90, ta duba hukumomi da ma’aikatan da za a iya rusawa.
A lokacin da aka yi aikin nan, ma’aikatu da cibiyoyi 541 ake da su a tarayya, zuwa yanzu an kirkiro wasu sababbi kamar NDPB a 2022.
Aikin Oronsaye zai tashi kujerun hajji?
NCNE da UBEC za su koma hukuma daya kamar yadda za a yi wa NASENI da wata ma’aikata, watakila a gwama NCAC da wasunta.
Hukumomin NAHCON da NCPC za su tashi aiki, hakan yana nufin babu ruwan gwamnati da harkar alhazai da masu ziyarar kirista.
NTA, FRCN da VON duka za su shiga wata hukuma mai alhakin watsa labarai. AFIT da jami’ar sojoji za su zama ‘yaruwar makarantar NDA.
Sauran shawarwarin kwamitin Oronsaye
An bada shawarar ruguza FRC da NSIWC, a bar aikinsu a hannun RMAFC sai a hada CCB, EFCC da ICPC a cikin wata hukuma guda dabam.
NIPOST, NCC, NBC za su zama hukuma daya idan aka yi amfani da shawarar Oronsaye, sai canjin suna da aka yi wa CCB da FCSC.
Jerin ma'aikatun da za a soke ko su narke
1. FRC
2. FAAN
3. NSIWC,
4. CCB
5. EFCC
6. ICPC
7. PCC
8. NACA
9. NEMA
10. PCC
11. NACA
12. ICRC
13. NCAA
14. NOSDRA
15. NESREA
16. OGFZA
17. FERMA
18. NIPC
19. NCNE
20. NCAC
21. NASENI
22. FIIRO
23. PRODA
24. BCDA
25. RMRDC
26. NABDA
27. NNMDA
28. NAHCON
29. NCPC
30. NCC
31. NBC
32. NITDA
33. ECN
34. NIPOST
35. NALDA
36. NIDCOM
37. NCMM
38. DMO
39. NAPEP
40. PSIN
41. ASCON
42. NCDMB
43. NGSA
44. FAAN
45. UCC
CBN: 'Yan canji sun tsorata da Tinubu
‘Yan kasuwar canji musamman daga Arewa sun tsorata da sababbin ka’idojin da CBN ya fito da su, ana da labari suna ganin za a yake su ne.
Masu sana’ar saye da saida kudin ketare sun zargi Yemi Cordoso da nemin ganin bayansu. Akwai wadanda suka yabi sababbin dokokin.
Asali: Legit.ng