Gwamna Ya Yi Martani Yayin da Daliba a Gombe Ta Lashe Gasar Masabaka Ta Duniya a Jordan, an Yi Murna
- Gwamna Muhammad Yahaya na jihar Gombe ya nuna farin cikinsa da nasarar matashiya Hajara daga jihar a gasar musabaka ta duniya
- Gwamnan ya ce da zarar ta dawo daga kasar Jordan zai tarbe ta a ofishinsa wanda hakan zai karawa ‘yan baya kwarin gwiwa
- Legit Hausa ta ji ta bakin Hajara Ibrahim Dan'azumi wacce ta yi nasara a gasar musabaka ta duniya a ƙasar Jordan da aka gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Gombe – Wata matashiya a jihar Gombe mai suna Hajara Ibrahim Dan’azumi ta yi nasarar lashe gasar musabaka ta duniya a kasar Jordan.
Hajara wacce ke karartu a Jami’ar jihar Gombe ta yi nasara a musabakar ce bangaren mata da aka gudanar tsakanin kasashe 39 na duniya.
Yadda Hajara ta samu nasara a gasar
Dan’azumi wacce ta fito daga Islamiyyar Abubakar Siddiq a Gombe ta samu maki 99.5 a gasar ta izu 60 da aka yi tsakanin ranakun 17 zuwa 22 ga watan Faburairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan nasara ta matashiyar ta samu yabo daga dukkan bangarorin kasar baki daya ganin yadda ta yi abin da ba a taba yi ba a jihar.
A martaninsa, Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya taya matashiyar murna da iyalanta da kuma malamanta gaba daya.
Martanin Gwamna Inuwa kan nasarar
Babban daraktan yada labaran gwamna a bangaren yada labarai, Isma’ila Uba Misilli shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa.
Inuwa ya ce wannan nasara ta Hajara zai zama karin karfin gwiwa ga ‘yan baya inda ya ce ya yi matukar jin dadi kan wannan nasara.
A cewarsa:
“Na yi matukar farin ciki da kuma alfahari da Hajara, wannan nasara ya kara mana daraja ba iya Gombe ba har Najeriya gaba daya.
“Ina da tabbacin wannan nasara tata za ta kara wa ‘yan baya karfin gwiwa musamman ‘ya’ya mata.”
Yayin da ake saran gwamnan zai tarbe ta a cikin ofishinsa da ke gidan gwamnati inda ya ce hakan zai karawa wasu kwarin gwiwa.
Legit Hausa ta ji ta bakin Hajara wacce ta yi nasara ga gasar musabaka ta duniya a ƙasar Jordan.
Hajara ta fara da godiya ga Ubangiji da ya ba ta wannan dama da ta samu na farin cikitare da godiya ga iyayenta.
Ta ce:
"Da farko ina godiya ga Ubangiji da ya bani wannan dama na yi nasara wanda addu'o'in da muke yi su ne Allah ya karba.
"Ina godewa ga iyayena da suka ba ni tarbiyya nagari suka tsaya don ganin nasamu haddar Alkur'ani mai girma da kuma samun wannan nasara."
Uba Sani ya yi alkawari ga masu musabaka
Kun ji cewa Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin kujerar hajji ga wandanda suka lashe gasar musabaka.
Sani ya ce kyautar za ta shafi dukkan bangarorin mata da maza wanda hakan zai kara musu kokari.
Asali: Legit.ng