Dan Najeriya ya ci gagarumar kyauta a musabaka a kasar Iran

Dan Najeriya ya ci gagarumar kyauta a musabaka a kasar Iran

- Wani dan Najeriya ya taya abokinsa murna bisa kyautar da ya kashe a gasar hadar Kur'ani da akayi a kasar Iran

- Mutumin yayi amfani da shafinsa na Twitter, Al-Hafiz inda ya nuna wa duniya hotunan kyaututukan da abokinsa ya samu saboda zuwa na uku a gasar

- Matashin da yayi hazakar, Goni Tijjani Goni Mohammad Dan Baba, dan asalin jihar Yobe ne a Nakjeriya

Legit.ng tayi karo da wani mutum mai suna Al-Hafiz Nafiu wanda yayi amfani da shafi sada zumunta na Twitter ya taya abokinsa murnar kasancewa zakara na biyu a gasar hadar Kur'ani da aka kammala a kasar Iran. Al-Hafiz ya nuna hotunan dake nuna abokinsa yayinda ya ke karbar kyaututukan da ya lashe.

Musabaqar da aka gudanar a kasar Iran ya samu hallarcin masana Kur'ani daga kasashen duniya da dama amma Goni Tijjani Goni Muhammad Dan Baba wanda dan asalin jihar Yobe ne ya zamo na uku cikin duk sauran wanda suka hallarci musabaqar.

Wani dan Najeriya ya nuna hazaka sosai a gasar karatun Kur'ani a kasar Iraqi
Wani dan Najeriya ya nuna hazaka sosai a gasar karatun Kur'ani a kasar Iraqi

Abin sha'awa a nan shine yadda Tijjani ya kara da sauran mahallarta musabaqar daga kasashe na duniya amma duk da haka ya nuna hazaka inda ya zamo na uku a duniya, hakan kuma yasa yan uwa musulmi yan Najeriya sunyi alfahari dashi.

Ga abinda Hafiz ya rubuta a shafinsa na Twitter tare da hotunan abokinsa:

"Ina taya abokina Goni Tijjani Goni Muhammad Dan Baba dan jihar Yobe bisa nasarar da yayi a gasar haddar Kur'ani na kasa-da-kasa da akayi a kasar Iran. Ina taya sauran yan Najeriya murna."

Dan Najeriya ya ci gagarumar kyauta a musabaka a kasar Iran
Dan Najeriya ya ci gagarumar kyauta a musabaka a kasar Iran

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: