Faduwar Darajar Naira Ta Taba Dukiyar Dangote, Ya Sauka a Matsayinsa a Jerin Attajiran Duniya
- Aliko Dangote ya yi asarar kimanin dala biliyan 3 a watan Fabrairu bayan da gwamnatin Najeriya ta karya darajar Naira
- Hamshakin attajirin nan na Najeriya ya yi asarar sama da dala biliyan 7 daga dukiyarsa yayin da Naira ta yi kasa a darajarta
- Adadin kudin Dangote a halin yanzu ya kai kimanin dala biliyan 14.8, kuma ya kasance a matsayi na 132 a jerin masu kudi a duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, ya yi asarar kimanin dala biliyan 3 a makon da ya gabata yayin da Najeriya ta fara rage darajar Naira a karo na biyu.
Attajirin dan Najeriya na daya daga cikin wadanda faduwar darajar Naira ya fi shafa, domin ya yi asarar kusan dala biliyan bakwai tun watan Janairu.
Yadda dukiyar attajiri Dangote ta ragu
Alkaluman Bloomberg sun nuna cewa a halin yanzu dukiyar Dangote ta kai dala biliyan 14.8, inda ta ragu da dala biliyan 3 a mako na biyu na watan Fabrairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya fara farfadowa ne a watan Janairu, inda ya samu dalar Amurka biliyan 7 cikin makonni tare da zama na na 82 a duniya.
Sai dai, daga baya ya yi kasa zuwa matsayi na 132 a jerin attajiran duniya bayan da Najeriya ta karya darajar kudinta zuwa wani mummunan daraja.
Duk da kyakykyawan sakamakon da kamfanin Dangote na siminti, wanda shine tushen arzikinsa, attajirin na ta samun nakasu a karuwar adadin dukiya.
Dangote ya yi asarar kusan dala biliyan 7 a cikin wata daya
A karshen watan Janairun 2024, arzikin Dangote ya kai dala biliyan 22, adadin mafi yawa da ya tara a cikin shekaru 10.
Duk da haka, ya yi asarar kusan kashi daya bisa hudu na dukiyarsa, sakamakon kudurorin gwamnatin Najeriya, wanda hakan ya kawo cikas ga nasarorin da kamfanin simintinsa ya samu.
Kamfanin simitin Dangote ya zama kamfani mafi kawo riba a Najeriya bayan da ya samu Naira tiriliyan 13 a darajar kasuwa a watan Fabrairun 2024.
Farashin simintin Dangote ya kai N11,000 a jihar Legas
A wani rahoton kuma, kun ji yadda farashin simintin Dangote ya kara tashi a kasuwa sama da yadda aka saba siya.
Idan baku manta ba, an samu tashin kayayyaki a kasar, wanda siminti na daga cikin abubuwan da suka kara kudi baktatan.
Sai dai, wasu ‘yan Najeriya sun bayyana yadda suke siyan simintin a farashin da ya yi kasa da N8,000 a wasu jihohin kasar.
Asali: Legit.ng